in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban jami'in MDD ya nuna damuwa game da karuwar tashin hankali a yammacin hamadar sahara
2018-01-07 13:52:55 cri
Babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya nuna damuwa game da karuwar tashin hankali a yankin shinge da aka kafa yammacin hamadar sahara inda ya bukaci a shawo kan al'amurran.

A ta bakin kakakinsa Farhan Haq, sakatare janar na MDDr ya yi matukar nuna juyayi sakamakon karuwar zaman tankiya na baya bayan nan a yankin Guerguerat a kudancin yankin yammacin hamadar sahara tsakanin iyakokin kasashen Morocco da Mauritaniya.

Mista Guterres yace janye dakarun mayakan Frente Polisario daga yankin Guerguerat a watan Afrilun shekarar 2017, tare da kuma da yunkurin janye dakarun kasar Morocco daga yankin, zai bada damar samar da kyakkyawan yanayin da za'a samu damar sake dawowa teburin tattaunawar sulhu karkashin wakilin musamman na sakataren MDD Horst Kohler.

Sakatare janar din ya bukaci dukkan bangarorin dasu kai zuciya nesa su guji duk wani abu da zai yi sanadiyyar kara dagula al'amurra a yankin.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China