An ce, an yi binciken ne a kasashe 22 dake fadin duniya, kuma yawan mutanen da aka yi binciken a kan su ya kai mutum 11000. Rahoton ya bayyana cewa, kashi 60 cikin dari na mutanen da aka yi binciken a kan su a kasashen waje sun amince da cewa kasar Sin ta fi taka muhimmiyar rawa a kan tsarin hadin gwiwar kasashen BRICS, kana suna fatan kasar Sin za ta kara samar da gudummawa a wannan fanni.
Kaza lika al'adun kasar Sin, da abincin irin na Sin, da maganin gargajiya na Sin, da kuma wasan Gongfu na sahun gaba a wakilcin al'adun kasar Sin.
Har ila yau kuma, rahoton ya yi nuni da cewa, kashi 59 cikin dari na mutanen da aka yi binciken da su, sun yabawa karfin kirkire-kirkire a fannin kimiyya da fasaha na kasar Sin. A hannu guda kuma jirgin kasa mafi sauri ya kasance muhimmin abun da Sin ta kirkiro a idanun al'ummun kasa da kasa. (Zainab)