in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Adadin neman samun ikon mallakar fasaha a Sin a 2017 ya kai miliyan 1 da dubu 382
2018-01-05 11:16:16 cri

Jiya Alhamis aka shirya taron shugabannin hukumomin kula da ikon mallakar fasaha na fadin kasar Sin a shekarar 2018 a nan birnin Beijing, inda aka bayyana cewa, a shekarar 2017 da ta gabata, gaba daya adadin neman samun ikon mallakar fasaha da aka gabatar a kasar ta Sin ya kai miliyan 1 da dubu 382, adadin da ya karu da kaso 14.2 bisa dari, idan aka kwatanta da shekarar 2016. A sa'i daya kuma, kasar Sin ta nuna kwazo da himma a fannin kara karfafa hadin gwiwar dake tsakaninta da sauran kasashen duniya, har ta daddale yarjejeniyoyin hadin gwiwa tsakanin sassa biyu ko sassa da dama a fannin, wanda yawansu ya kai 52 a shekarar bara da ta gabata. A shekarar 2018 kuwa, kasar Sin za ta kara himmantu kan wannan aiki domin kara samun ci gaba.

Yayin taron da aka gudanar jiya, shugaban babbar hukumar kula da ikon mallakar fasaha ta kasar Sin Shen Changyu ya bayyana cewa, a shekarar 2017, adadin neman samun ikon mallakar fasaha a kasar Sin da adadin ikon mallakar fasaha da aka samu a kasar sun karu bisa babban mataki, kana aikin kare ikon mallakar fasaha ya samu kyautatuwa a bayyane, ya ce, "A shekarar 2017, adadin neman samun mallakar fasaha da aka gabatar a kasar Sin ya kai miliyan 1 da dubu 382, adadin da ya karu da kaso 14.2 bisa dari idan aka kwatanta da na shekarar 2016, kuma adadin ayyukan dudduba takardun neman samun ikon mallakar fasaha da suka kammala ya kai dubu 744, wato an kai ga kammala aikin cikin watanni 22. Ban da haka kuma, bisa alkaluman da aka samu, an ce, a babban yankin kasar Sin, wato ban da Hongkong da Macau da kuma Taiwan, gaba daya adadin ikon mallakar fasahar da aka samu ya kai miliyan 1 da dubu 356, wato adadin ya kai 9.8 bisa dari cikin mutane dubu goma. Ban da haka kuma, adadin kudin da aka tattara ta hanyar yin mafani da ikon mallakar fasaha ya kai kudin Sin yuan biliyan 72, adadin da ya karu da kaso 65 bisa dari idan aka kwatanta da shekarar 2016. Kaza lika, adadin kudin da aka samu daga fitar da ikon mallakar fasaha zuwa ga kasashen ketare ya zarta dalar Amurka biliyan 1."

Shen Changyu ya ci gaba da cewa, a cikin 'yan shekarun da suka gabata, kasar Sin ita ma ta samu babban sakamako wajen gudanar da hadin gwiwa tsakaninta da sauran kasashen duniya, yanzu kasar Sin ta riga ta fara gudanar da aikin dudduba takardun neman samun ikon mallakar fasaha cikin sauri tsakaninta da sauran kasashe 23. Ta daddale yarjejeniyoyin hadin gwiwa dake tsakanin sassa biyu ko sassa da dama a fannin da yawansu ya kai 52. Ya ce, "Yayin taron kolin da aka shirya domin gudanar da hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa kan shawarar ziri daya da hanya daya, babbar hukumar kula da ikon mallakar fasaha ta kasar Sin ta daddale yarjejeniyar hadin gwiwa da hukumar kula da ikon mallakar fasaha ta duniya a madadin gwamnatin kasar Sin, kuma sassan biyu sun daddale yarjejeniyar fahimtar juna game da yin hayar ma'aikatan kasar Sin ta hanyar kafa asusu na musamman. Ban da haka kuma, kasar Sin za kara karfafa hadin gwiwa tsakaninta da kasashen duniya daga duk fannoni, musamman ma tsakaninta da kasashen BRICS, Hukumar kula da ikon mallakar fasaha ta kasar Sin za ta kafa huldar abokantaka bisa manyan tsare tsare daga duk fannoni da hukumar kula da ikon mallakar fasaha ta Turai. Abu mai faranta ran mutane shi ne kasar Kambodiya, ta kasance kasa ta farko wadda ta amince da ikon mallakar fasaha na kasar Sin a kasarta."

A shekarar bana, kasar Sin za ta mai da hankali kan ingancin ikon mallakar fasaha, Shen Changyu ya ce, "Kasar Sin za ta mai da hankali kan ingancin ikon mallakar fasaha ta hanyar sa kaimi kan kirkire kirkiren fasahar zamani, wanda da haka kuma ikon mallakar fasaha na kasar Sin zai kai ma'aunin kasashen duniya."

Babbar hukumar kula da ikon mallakar fasaha ta kasar Sin ta fayyace cewa, kasar ta Sin za ta sa kaimi kan ci gaban aikin neman samun ikon mallakar fasaha a shekarar 2018, kuma an kimanta cewa, adadin zai karu da kaso 7 bisa dari. (Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China