in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta kaddamar da dandalin karbar rance ta yanar gizo na farko
2018-01-05 11:12:36 cri
Kamfanoni da dama masu hidimar bada intanet ne suka mikawa babban bankin kasar Sin bukatar kafa wani dandalin karbar rance.

A cewar bankin al'ummar kasar Sin, sabon kamfanin mai suna Baihang Credit Scoring, zai samu goyon baya daga kamfanin Alibaba da Tencent da sauran wasu kamanoni.

Kungiyar samar da kudaden bada hidimar Intane ta kasar Sin ita ce za ta zama babbar mai hannu jari a kamfanin da kaso 36.

Za a yi wa kamfanin Baihang rejista da jarin yuan biliyan 1, kwatankwacin dala miliyan 150. Kamfanonin bada rance 8 ciki har da Zhima da Tencent za su mallaki kashi 8 kowannensu, na hannun jarin kamfanin, inda Zhu Huanqi shugaban kamfanin Huida zai Jagorancin sabon kamfanin.

Kamfanin zai samar da bayanan bada rance ga masu bukata ta yanar gizo, domin taimakawa kamfanoni gwamnati dake makamancin aikin. (Fa'iza)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China