A baya-bayan nan ne tarayyar ta sanar da cewa, za ta gudanar da taron gama gari na shugabannin kasashe da Gwamnatocin Afrika karo na 30, daga ranar 22 zuwa 29 ga wannan wata a hedkwatarta dake Addis Ababa babban birnin Habasha.
Taron da aka yi wa taken 'nasarar yaki da cin hanci: hanya mafi dorewa ta sauya nahiyar Afrika', ya ja hankalin masana da kwararru saboda tasirin da zai yi ga ci gaban nahiyar baki daya.
A jawabinsa na sabuwar shekara, shugaban hukumar kula da ayyukan AU Moussa Faki Mahamat, ya ce yaki da cin hanci shi ne jigon ci gaban nahiyar da kawar da bambamci a tsakanin al'ummarta.
A cewarsa, cin hanci ya haifar da rashin daidaito tsakanin al'ummomin tare da keta dokoki a nahiyar, ya na mai cewa duk da shaidu sun nuna cewa cikin shekaru 5 da suka gabata, nahiyar ta dauki matakai masu karfafa gwiwa, har yanzu da sauran rina a kaba.
Har ila yau, Moussa Faki Mahamat ya ce a kokarin magance manyan kalubalen da cin hanci ya haifar a nahiyar, zauren tarayya ya ayyana shekarar 2018 a matsayin shekarar yaki da cin hanci ta nahiyar Afrika mai taken 'nasarar yaki da cin hanci: hanya mafi dorewa ta sauya nahiyar Afrika'. (Fa'iza Mustapha)