in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta fara aiwatar da dokar haraji kan kare muhalli
2018-01-04 11:10:25 cri


Tun daga ranar 1 ga watan Janairun bana, kasar Sin ta fara aiwatar da dokar haraji kan kare muhalli, wadda ta kasance dokar haraji ta farko da kasar ta bullo da ita ta fuskar kare muhallin halittunta. Bisa wannan doka, gwamnatin kasar Sin za ta ci tarar kamfanonin da suke fitar da abubuwa masu gurbata iska da ruwa da karar injuna masu damun mutane. Masana sun ce, aiwatar da irin wannan doka zai tilastawa kamfanoni su yin gyare-gyare kan ayyukan da suke yi, abun da zai kara kyautata tsarinsu.

Aiwatar da dokar haraji kan kare muhalli, na shaida cewa, kasar Sin ta kawo karshen tsarin karbar kudade kan aikace-aikacen dake gurbata muhalli, wanda aka shafe tsawon shekaru kusan arba'in ana amfani da shi. A nata ra'ayi, wata babbar malama mai nazarin ilimin muhalli daga jami'ar Renmin ta kasar Sin, Lan Hong ta ce, dokar haraji kan kare muhalli ta fi dacewa da halin da ake ciki yanzu a kasar Sin, idan aka kwatanta da tsarin karbar kudade kan aikace-aikacen gurbata muhalli. Madam Lan ta ce:

"Dokar haraji kan kare muhalli ta fi karfi, idan aka kwatanta da tsohon tsarin karbar kudade kan aikace-aikacen dake gurbata muhalli. Idan kamfanoni ba su biya haraji ba, to sun keta doka. Amma a da, idan ba su biya tara kan aikace-aikacen fitar da abubuwa masu gurbata muhalli ba, ba su sabawa doka ba, keta ka'ida ne kawai. Don haka wannan sabuwar doka za ta fi tasirin a kan kamfanoni."

Game da yadda za'a yi domin buga harajin, shugaban sashin tsara manufofi da dokoki na ma'aikatar kare muhalli ta kasar Sin, Mista Bie Tao ya bayyana cewa:

"Bisa dokar haraji kan kare muhalli, matakan da za'a bi domin tattaro haraji sun hada da, na farko gwamnatin lardi za ta bullo da matakan buga haraji, daga bisani, ta gabatar da su ga majalisar dokokin lardin don samun amincewa, haka kuma za ta gabatar da su ga majalisar dokokin kasa gami da majalisar gudanarwa ta kasar Sin don su tantance. Wata muhimmiyar ka'ida ita ce, idan kamfanoni suka fitar da abubuwa masu gurbata muhalli masu dimbin yawa, za su biya haraji mai yawa. Amma idan suka fitar da abubuwa kalilan, ba za su biya haraji mai yawa ba. Alal misali, idan yawan abubuwa masu gurbata muhalli da wani kamfani ya fitar ya yi kasa da kashi 50 bisa dari na ma'auni harajin, to za'a rage rabin harajin da zai biya. Idan yawan abubuwa masu gurbata muhalli da kamfanin ya fitar ya yi kasa da kashi 30 bisa dari, to za'a buga masa haraji na kashi 75 bisa dari."

Bisa dokar haraji kan kare muhalli, za'a buga haraji kan aikace-aikace da dama masu gurbata muhallin halittu, ciki har da fitar da abubuwa masu gurbata muhalli zuwa ga iska, da ruwa, ko kuma fitar da karar injuna masu damun mutane. Mutanen da za su biya harajin, sun hada da, kamfanonin da suke fitar da abubuwa masu gurbata muhalli kai-tsaye zuwa ga muhalli. Hakan na nufin cewa, idan kamfanoni ba su fitar da abubuwa masu gurbata muhalli kai-tsaye ba, to babu bukatar su biya haraji. Haka kuma dan Adam shi kansa, babu bukatar ya biya haraji.

Mataimakin shugaban sashin nazarin albarkatu da muhalli na cibiyar nazarin harkokin ci gaba ta majalisar gudanarwar kasar Sin, Mista Chang Jiwen ya bayyana cewa, ma'aunin tara haraji a sassa daban-daban na kasar Sin ya sha bamban sosai. A wasu lardunan kasar Sin, ciki har da Liaoning da Jilin da Anhui da Xinjiang, kamfanoni su kan biya haraji bisa ma'auni mafi kankanta, amma a Beijing da Tianjin da Hebei da kuma Shanghai, kamfanoni su kan biya karin haraji, musamman ma babban birnin Beijing. Manazarta na hasashen cewa, yawan kudin harajin da za'a tara a duk shekara zai kai kudin Sin Yuan biliyan hamsin.

Chang Jiwen ya ce, aiwatar da dokar haraji kan kare muhalli zai taka rawar gani ga yin gyare-gyare ga tsarin masana'antun kasar Sin, inda ya ce:

"Cikin nan da shekara daya ko biyu masu zuwa da fara aiwatar da wannan doka, za ta yi tasiri ga tattalin arzikin kasar Sin, musamman masana'antun da suke gurbata muhalli. Ya zama dole wasu kamfanoni su yi taka-tsantsan, musamman kamfanonin dake fitar da abubuwa masu gurbata iska da ruwa da karar injuna masu damun mutane da sauransu. Adadin yawan harajin da kamfanoni za su biya ya fi na da, shi ya sa, aka tilasta wa kamfanonin gaggauta yin kwaskwarima ga ayyukansu, da kara maida hankali kan ayyukan kare muhalli. Don haka a ganina, aiwatar da wannan doka zai taka muhimmiyar rawa ga kyautata tsarin masana'antu gami da kare muhallin halittu na kasar Sin."(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China