in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aikatar yawon bude idon kasar Uganda ta yabawa Sin game da haram cinikin hauren giwa
2018-01-04 10:26:16 cri
Ma'aikatar yawon bude idon kasar Uganda ta yi na'am da matakin da kasar Sin ta dauka na aiwatar da shirin haramta cinikin hauren giwaye, inda ta bayyana matakin da cewa ya kasance abin yabo.

Ephraim Kamuntu, ministan yawon bude ido da kula da gandun daji na kasar Uganda, ya shedawa kamfanin dillancin labaran Xinhua cewa, cinikin hauren giwaye batu ne da aka jima ana gudanar da shi a duniya ba tare da an haramta shi ba.

A ranar 31 ga watan Disambar 2017, kasar Sin ta rufe kofarta a hukumance, inda ta haramta cinikin hauren giwaye, ta kuma ayyana duk wani batu da ya shafi saye da sayarwa na dukkan abubuwan da ake sarrafawa daga hauren giwa a matsayin haramtacce a fadin kasar ta nahiyar Asiya.

Minista Kamuntu ya bayyana cewa, "Wannan abin farin ciki ne. Haramta cinikin hauren giwaye da aiwatar da shi abu ne da ya kamata a aiwatar da shi tun da jimawa. Wannan babban cigaba ne ga kasar Sin. Kasar Uganda, kamar yadda aka sani, muna da giwaye kuma masu farautarsu suna hallakasu domin neman haure". (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China