in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Ghana zai kafa ofishi na musamman na yaki da rashawa
2018-01-03 13:43:25 cri
Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo ya dauki muhimmin mataki na yaki da rashawa inda ya amince da shirin dokar da zai bada damar kafa ofishi na musamman na bincike game da ayyukan rashawa wato OSP.

Makasudin kafa ofishin na OSP shi ne, domin ya kasance a matsayin hukuma ta musamman wadda zata dinga bincikar jami'an gwamnati da ake zargi da aikata rashawa, da 'yan siyasa, har ma da ma'aikatan dake hukumomi masu zaman kansu wadanda ke da hannu wajen aikata rashawa, hukumar zata gabatar da laifukan ne ga ofishin Atoni janar na kasar.

Akufo-Addo, ya fada a lokacin kwarya-kwaryar bikin sanya hannu kan shirin a gidan gwamnatin kasar dake Accra, yace babban abinda yake fata shine, kafa ofishin zai kasance a matsayin wani muhimmin mataki a burin da yake dashi na kakkabe ayyukan rashawa a tsarin ayyukan gwamnatin kasar Ghanan.

Yace cin hanci shine babban abin dake dakile cigaban kasar ta Ghana, kuma yana fata wannan ofishi zai tabbatar da ganin tsoffin jami'an gwamnati da na yanzu, ana bincikarsu game da yadda suka tafiyar da sha'anin ayyukan gwamnati, kana yace ba za'a taba barin ayyukan rashawa su wuce ba tare da bincike ba.

Kafa ofishin na OSP na daya daga cikin alkawuran da shugaban yayi a lokacin yakin neman zabe na jamiyyar (NPP) mai mulkin kasar.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China