in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta kara gina layin dogo mai saurin gaske na tsawon kilomita 3500 a bana
2018-01-03 10:43:51 cri

Jiya Talata ne, hukumar kula da layin dogo ta kasar Sin ta shirya taro a nan birnin Beijing, inda babban manajan hukumar Lu Dongfu ya gabatar da jawabin aikinsa yayin taron, Yana mai cewa, a shekarar da ta gabata, gaba daya adadin jarin da aka zuba a aikin gina layin dogo a nan kasar Sin ya kai RMB yuan biliyan 801, kuma an yi amfani da kudaden ne domin gina sabbin layukan da suka tsawon kilomita 3038. Sannan a bana kasar Sin za ta kara zuba jari domin gina layin dogo da ya kai tsawon kilomita 3500.

A makon da ya gabata ne, layin dogo mai saurin gaske da aka gina tsakanin birnin Shijiazhuang na lardin Hebei da birnin Jinan na lardin Shandong ya fara aiki, wani fasinja wanda ya shiga jirgin ya gaya mana cewa, sun ji dadi matuka tun bayan da wannan layin dogon ya fara aiki, ya ce, "Sabon jirgin kasan ya fi sauri kuma ya fi dadi idan aka kwatanta shi da tsohon layin, lokacin da ake dauka a kan hanya ya ragu da kusan rabi."

A shekarar 2017 da ta wuce, gaba daya adadin jarin da aka zuba kan aikin gina layin dogo a nan kasar Sin ya kai RMB yuan biliyan 801,kuma an yi amfani da kudaden ne wajen gina layin dogo mai sauri tsakanin birnin Baoji na lardin Shaanxi da birnin Lanzhou na lardin Gansu da layin dogo mai saurin gaske tsakanin birnin Xi'an na lardin Shaanxi da birnin Chengdu na lardin Sichuan da layin dogo mai sauri tafiya tsakanin birnin Shijiazhuang na lardin Hebei da birnin Jinan na lardin Shandong da sauransu, gaba daya tsawonsu ya kai kilomita 3038, a sa'i daya kuma, fasahar gina layin dogo na kasar Sin ita ma ta shiga wani sabon mataki, babban manajan kamfanin jirgin kasan kasar Sin Lu Dongfu ya yi mana bayani cewa, "Ana kara kyautata tsarin fasahohin aikinmu a fannoni uku misali gina layin dogo da kera na'urorin da abin ya shafa da kuma gudanar da harkokin dake shafar layin dogo,wanda ya kasance a sahun gaba a fadin duniya, a halin da ake ciki yanzu, saurin jirgin kasan kasar Sin mai saurin gaske ya kai kilomita 350 a ko wace sa'a, saurin da ya kasance a sahun gaba a duniya."

Ban da haka kuma, a shekarar bara wato 2017 da ta gabata, gaba daya adadin fasinjojin da jiragen kasa suka jigilar su ya kai biliyan 3 da miliyan 39, adadin da ya karu da kaso 9.6 bisa dari idan aka kwatanta da na shekarar 2016, kana adadin kayayyakin da aka jigilar su ta jiragen kasa ya kai tan biliyan 2 da miliyan 918, adadin da ya karu da kaso 10.1 bisa dari idan aka kwatanta da na shekarar 2016, abu mafi muhimmanci shi ne ana gudanar da aikin cikin kwanciyar hankali, babu wani mummunan hadari da ya auku a duk tsawon shekarar ta 2017, wato babu fasinja ko daya da ya rasa ransa a jirgin kasan da ya shiga.

Babban manaja Lu Dongfu ya bayyana cewa, a shekarar 2018 da muke ciki, kasar Sin za ta kara mai da hankali kan ingancin aikin gina layin dogo, da hidimar da ake samarwa fasinja, ya ce, "Bana kasar Sin za ta zuba jarin da yawansa ya kai RMB yuan biliyan 732 domin gina sabbin layukan dogo da suka kai tsawon kilomita 4000 a kasar, a cikin wannan adadi, za a gina layin dogo mai saurin tafiya da ya kai tsawon kilomita 3500."

Yanzu haka a kasar Sin an cimma burin gina layin dogo mai saurin gaske kamar yanar gizo, nan gaba za a kara habaka aikin a fadin kasar, kana ana kara kyautata aikin samar da hidima mai inganci ga fasinjoji ta hanyoyi daban daban, misali, sayen tikiti ta intanet kafin lokaci.

Yayin taron da aka shirya jiya, babban manaja Lu Dongfu ya bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da yin kokari matuka domin kara zamanintar da layin dogo na kasar, ta yadda za ta cimma burinta na zama jagora a duniya nan da shekarar 2020, ya ce, "Ya zuwa shekarar 2020, ana sa ran za a cimma burin gina layin dogo na zamani a fadin kasar Sin, kuma tsawon layukan dogo a fadin kasar zai kai kilomita dubu 150, a ciki, tsawon layin dogo mai saurin gaske zai kai kilomita dubu 30."

Kazalika, kasar Sin za ta kara kokarin kyautata tsarin ma'aunin fasahar aikin gina layin dogo nan da shekarar 2020, musamman ma wajen gina layin dogo mai saurin gaske, da layin dogo na kan tudu, da layin dogo a yanki mai sanyin gaske, da layin dogon dakon kaya masu nauyi da sauransu.

Ya zuwa shekarar 2025 kuwa, kasar Sin za ta kara gina layin dogo da zai kai tsawon kilomita kusan dubu 175, wanda a ciki, tsawon layin dogo mai saurin gaske zai kai wajen kilomita dubu 38.(Jamila)


Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China