in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Nijeriya ya bayyana kudurorin gwamnatinsa a sabuwar shekarar 2018
2018-01-02 11:08:43 cri

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya ce tilas ne 'yan siyasa su kujewa sanya kabilanci da bambamcin addini cikin harkokin siyasa yayin da lokacin zabe a kasar ke karatowa.

Muhammadu Buhari ya bayyana haka ne a jawabinsa na sabuwar shekarar 2018 ga al'ummar kasar a Abuja babban birnin Nijeriya.

Da yake jawabi, Muhammadu Buhari ya jaddada cewa idan har 'yan Nijeriya suna son zaman lafiya, to ya kamata su kauracewa kazantacciyar siyasa.

A cewarsa ya kamata a rika gudanar da harkokin siyasa bisa wayewa da sanin ya kamata, kuma bisa tanadin kundin tsarin mulki, yana mai cewa karfafa tsarin demokradiyya da biyayya da kundin tsarin mulki, hakki ne da ya rataya a wuyan dukkan al'ummar kasar .

Nijeriya ta shirya gudanar da babban zabenta ne a watan Fabrairun badi.

Game da batun tsaro kuwa, shugaba Buhari, ya tabbatarwa al'ummar kasar cewa har yanzu, tsaron rayuka da dukiyar al'umma shi ne babban abun da gwamnatinsa ta ba muhimmanci.

A cewarsa, ta'addanci da sauran manyan laifuka abu ne da ke aukuwa a duniya baki daya, kuma jami'an tsaro na ci gaba da daukar matakan da suka dace na tunkarar duk wata barazana.

Daga bangaren ababen more rayuwa, shugaba Muhammadu Buhari ya ce Gwamnatinsa ta kammala shirye-shiryen inganta sufurin jiragen kasa a dukkanin yankunan kasar a shekarar 2018.

Ya ce aikin layin dogon da ya tashi daga Lagos zuwa Kano wanda zai iya daukar fasinjoji miliyan biyu a ko wace shekara tare da kayayyaki ton miliyan 5, zai kai birnin Badan daga Lagos din a karshen shekarar 2019. Haka zalika shimfida layin dogon da ya hada Kano da Kaduna da ake san ran farawa a bana, zai isa Kaduna zuwa karshen shekarar 2019.

A cewarsa, za a kara bunkasa layin dogon da ya hada biranen Abuja da Kaduna ta hanyar kara jirgi, ta yadda zai iya jigilar fasinjoji miliyan 1 cikin shekara 1.

Ya ce Gwamnatinsa ta kuduri niyyar hada karin wasu biranen ta hanyar shimfida layin dogo na zamani cikin shekaru kalilan masu zuwa, domin bunkasa yanayin rayuwa da tattalin arzikin al'umma.

Ya kara da cewa, aikin shimfida layin dogo mai sauri a cikin birnin Abuja ya kai kashi 98 na kammaluwa daga kashi 64 da ya kasance a shekarar 2015.

A cewarsa, sufurin jiragen kasa zai karfafa harkokin tattalin arziki a babban birnin tarayya tare da samarwa mazauna hanyar sufuri mafi aminci.

Bugu da kari, shugaban na Nijeriya Muhammadu Buhari, ya kuma sanar da cewa kasar za ta daina shigar da shinkafa a bana, domin karfafawa manoma na cikin gida.

Ya ce ya zama wajibi 'yan Nijeriya su zamo masu da'a da tsari ta fuskar kula da tattalin arziki domin lokacin magudi na gab da gushewa.

Shugaba Buhari ya kara da cewa, ya yi farin ciki da farfadowar harkokin gona, wanda ke bada gudunmuwa ga kokarin gwamnati na sake fasalin tsarin tattalin arziki.

Inda kuma ya yi kira ga 'yan kasuwa dake da basira da wadanda suka kammala karatu babu aikin yi da sauran mutane maza da mata masu jini a jika da basira da ilimi, da kada su yi zaman jiran aiki daga gwamnati ko kamfanoni.

A cewarsa, ana samun manyan kasashe ne idan mutane masu basira suka yi amfani da duk wata dama da ta zo musu, yana mai cewa Gwamnatinsa ta APC na kokarin saita tattalin arzikin kasar a hankali.

Muhammadu Buhari, ya ce kokarin baza komar tattalin arziki da Gwamnati ke yi, ya kawo kyakkyawan sakamako, musammam a bangarorin noma da ma'adinai.

Sai dai, shugaban ya bayyana takaici game da yadda al'umma ke wahala ba gaira ba dalili a lokacin bikin kirismeti da sabuwar shekara saboda karancin man fetur a fadin kasar, inda ya dora laifin a kan wasu daidaikun mutane masu son kai dake aiki a bangaren mai da iskar gas.

Ya jaddada aniyar Gwamnatinsa ta kawo karshen matsalar tare da tabbatar da dakatar da dukkan wadanda ke da hannu wajen samar da matsalar daga yin haka a nan gaba.

Haka zalika, shugaba Buhari wanda ya ce kamfanin mai na kasar NNPC, ya dauki matakan samar da man a dukkannin depo-depo dake kasar, ya ce ayyukan irin wadanan mutane marasa kishin kasa ba zai dauke hankalin Gwamnatinsa daga kudurinta na inganta rayuwar jama'a ba.

A nasa bangaren, Manajan Daraktan Kamafanin NNPC Maikanti Baru, ya dora laifin a kan dillalan man, inda ya ce jita-jitar kara farashin man ya sanya wasu dillalai boye man da suke da shi domin amfana daga Karin farashin.

Ya kuma tabbatarwa al'ummar kasar cewa, kamfanin ya rubanya yawan man da yake bayarwa daga lita miliyan 27 zuwa miliyan 30 a ko wace rana, zuwa lita miliyan 80, tun bayan da aka lura da karancin man.

Har ila yau, ya ce kamfanin na da isasshen mai da zai kai kwanaki 30 kuma nan ba da dadewa ba, matsalar za ta kau.

Karancin man fetur yayin bukukuwa dai, abu ne dake aukuwa a kasar duk shekara, duk da cewa bai faru ba cikin shekaru 2 da suka gabata. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China