in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An gudanar da taron kwamitin koli na jam'iyyar kwaminis ta Sin kan aikin raya kauyuka
2017-12-29 20:28:45 cri
An gudanar da taron kwamitin koli na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin kan aikin raya kauyuka tun daga ranar 28 zuwa 29 ga wata a nan birnin Beijing.

A yayin taron, an bayyana cewa, bayan kammala taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18 a shekarar 2012, kwamitin tsakiya na jam'iyyar a karkashin jagorancin Xi Jinping ya mai da aikin warware matsalolin aikin noma da manoma da kauyuka a matsayin muhimmin aikin jam'iyyar, kuma an samu nasarori tare da aiwatar da kwaskwarima kan yadda za a bunkasa aikin noma da raya kauyuka, wanda ya taimaka ga raya sha'anin jam'iyyar kwaminis da ma kasar Sin.

An bude wani sabon babi kan aikin yaki da talauci, da gudanar da manufofin yaki da talauci kamar yadda ake bukatu yadda ya kamata, matakin da kai ga tsame mutane fiye da miliyan 66 daga kangin talauci, da kuma nasarori a aikin yaki da talauci.

Haka kuma, a yayin taron an gabatar da burin raya kauyuka da ka'idojin gudanar da aikin. Bayanai na cewa, ya zuwa shekarar 2020, za a bullo da wasu manufofi a wannan fanni. Kana ya zuwa shekarar 2035, za a cimma burin zamanintar da aikin noma da raya kauyuka. Sannan ya zuwa shekarar 2050, za a cimma burin bunkasa kauyuka da aikin noma da kawo wadata ga manoma a dukkan fannoni. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China