in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
CRI da People's Daily sun fidda sakamakon zaben manyan labarai na kasa da kasa 10 na 2017 cikin hadin gwiwa
2017-12-29 10:12:09 cri
A yau Jumma'a 29 ga wata, Gidan Rediyon CRI da jaridar People's Daily, sun fidda sakamakon zaben manyan labarai na kasa da kasa guda 10 na shekarar 2017 cikin hadin gwiwa. Wadannan labarai guda 10 dai su ne:

1. Ra'ayin kasar Sin na samun amincewa daga gamayyar kasa da kasa, inda ake aiwatar da daftarin kasar Sin cikin kasa da kasa

2. Ficewar Amurka daga yarjejeniyoyin kasa da kasa na nuna manufar son kai da kasar ta dauka, da tsai da kudurori bisa moriyar kasar Amurka, wanda hakan ke bata tsarin gudanar da harkokin kasa da kasa

3. Karuwar gwajin makaman nukiliya a Koriya ta Arewa, ya haddasa tabarbarewar yanayin zaman lafiya a zirin Koriya

4. Abu ne mai wahala a iya aiwatar da manufofin ficewar Burtaniya daga kungiyar EU, wanda hakan ke haddasa illa ga dunkulewar kasashen Turai

5. Ganawar shugabannin kasashen Sin da Amurka ta janyo hankulan kasa da kasa, inda suka cimma ra'ayi daya kan raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu cikin zaman karko

6. Qatar ta gamu da matsalar "yanke huldar diflomasiyya", lamarin da ya kara tashe-tashen hankula a yankin Gabas ta tsakiya

7. An sassauta yanayin tekun Kudu bisa dukkan fannoni, yayin da aka kulla daftarin yadda za a aiwatar da harkokin dake shafar tekun Kudancin kasar Sin

8. Tattalin arzikin duniya ya fara samun farfadowa daga tabarbarewar sha'anin kudin duniya

9. An cimma nasarar gudanar da cikakken zaman taron wakilan JKS karo na 19, inda aka fidda daftarin neman bunkasuwa wanda zai amfani kasa da kasa

10. An cimma nasarar yaki da kungiyar IS, amma ana ci gaba da fuskantar matsalolin yaki da ta'addanci

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China