in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masana na fatan Afrika za ta bude wani sabon babi na ci gaba a 2018
2017-12-29 09:27:35 cri

Yayin da sabuwar shekara ke karatowa, masana a kasar Ruwanda sun bayyana kyakkyawar fata game da makomar Afrika a shekarar 2018, duk kuwa da irin kalubalen da take fuskanta.

Da yake tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, wani mai sharhi kan al'amuran siyasa Ladislas Ngendahimana, ya ce nahiyar Afrika za ta shiga sabon babi, inda ya ce, al'ummar Afrika sun gano matsalolinsu, al'amarin da zai ba su damar lalubo mafita da kansu.

Shi kuwa babban jami'in bincike na cibiyar nazarin muhimman batutuwan kasa da bincike ta Ruwanda Gatete Ruhumuriza, cewa ya yi sauyawar harkokin siyasar duniya za ta ba Afrika karin dama ta shiga a dama da ita cikin al'amuran da suka shafi duniya.

A nasa bangaren, masani kan harkokin tattalin arziki Teddy Kaberuka, ya ce kasashen Afrika na shigar da kayayyaki daga kasashen waje fiye da wadanda suke fitarwa, wanda ya ce ya ba da gudunmuwa wajen dogaro da suka yi kan tallafi da suke samu daga ketare domin aiwatar da ayyuka.

Ya kuma bayyana damuwa game da yadda mafi yawan kasashen ke da albarkatu, sannan suke fitar da albarkatun maimakon sarrafawa don samar da kayayyakin da za a fitar waje.(Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China