in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin: Hadin gwiwa ita hanya daya tilo ta raya alakar dake tsakanin Sin da Amurka
2017-12-28 19:50:07 cri

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin tsaron kasar Ren Guoqiang, ya ce, tarihi ya nuna cewa, hanya daya rak ta bunkasa huldar dake tsakanin kasashen Sin da Amurka ita ce ta yin hadin gwiwa.

Ren wanda ya bayyana hakan Alhamis din nan yayin taron manema labarai da ya gudana a nan birnin Beijing, ya ce Sin da Amurka za su amfana da wannan hadin gwiwa maimakon yin fito na fito.

Kalaman nasa na zuwa ne, yayin da yake mayar da martani kan tambayar da aka yi masa game da manufofin tsaro na bayanan baya-bayan da Amurka ta wallafa, inda ta sanya kasar Sin cikin jerin abokan adawarta, ya ce, yana fatan Amurka za ta hada kai da kasar Sin a manyan batutuwan tsaro na kasa da kasa da na shiyya-shiyya.

Kasar Sin tana fatan Amurka za ta yi watsi da batun cacar baka da bahaguwar fahimtarta, sannan ta kasance mai fadin gaskiya game da Sin da sojojinta, kana ta taka rawar da ta dace wajen bunkasa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu da kuma sojojinsu. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China