in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Iyalai 200 na gudun hijira sakamakon farmaki daga mayakan IS a Kirkuk
2017-12-28 10:28:05 cri

Kimanin iyalai 200 ne suka kauracewa gidajen su, inda suke samun mafaka a sansanin 'yan gudun hijira na Tal al-Seibat dake lardin Salahudin a tsakiyar kasar Iraqi.

Rahotanni na cewa, a ranar Laraba mayakan IS sun kaddamar da hare hare a lardin Kirkuk, lamarin da ya sanya dubban jama'a tserewa zuwa sansanin na al-Seibat mai nisan kilomita 30 daga gabashin birnin Tikrit, fadar mulkin lardin Salahudin.

Wani jami'in gwamnatin karamar hukumar Alam da ya nemi a boye sunan sa, ya ce mafi yawan 'yan gudun hijirar sun fito ne daga garuruwan Ryadh, da Rashad da Abbasi, da kuma kauyukan dake Hawijah Pocket dake kudu maso yammacin lardin Kirkuk.

A ranar 9 ga watan Disamba ne dai firaministan kasar Iraqi Haider al-Abadi, ya bayyanawa duniya cewa, an samu nasarar kakkabe mayakan IS daga daukacin yankunan kasar sa. To sai dai kuma har yanzu, daidaikun mayakan da suka boye a wasu sassan kasar, da wadanda ke samun mafaka a yankunan Hamada, da masu wuyar shiga, na kai hare hare kan fararen hula da jami'an tsaro a wuraren da ke da karancin tsaro.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China