in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Zambia ya kori wani minista
2017-12-28 10:14:43 cri

Shugaban kasar Zambia Edgar Lungu, ya sauke ministan ma'aikatar tsare tsaren da bunkasa kasa Lucky Mulusa daga mukamin sa, ya kuma janye sunan sa daga wadanda za su kasance cikin majalissar zartaswar kasar. Sai dai sanarwa da kakakin shugaban kasar Amos Chanda ya fitar mai kunshe da hakan, ba ta fayyace dalilan da suka sanya shugaban kasar ya sauke Mulusa daga aiki ba.

Rahotanni sun bayyana cewa, a watan Oktobar da ya gabata, Mulusa ya fuskanci fushin jam'iyya mai mulki, bayan da kwatanta wasu motocin kashe gobara 42 da gwamnati ta sayo kan kudi har dalar Amurka miliyan 42 da kurar dakon kaya ko wilbaro.

Hakan dai ya sanya wasu masu fada a ji a jam'iyyar rubuta korafi, tare da sukar kalaman Mr. Mulusa zuwa ga shugaban kasar, suna masu bukatar a sauke shi daga mukamin sa.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China