in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tashar samar da lantarkin da Sin ta gina ta bunkasa lantarki a Botswana
2017-12-28 10:09:13 cri

Tashar samar da lantarki ta Morupule B da babban kamfanin kasar Sin CNEEC ya gina a kasar Botswana, ta yi matukar bunkasa lantarki a fadin kasar, kamar yadda hukumar kididdiga ta kasar Botswanan ta sanar.

Cikin alkaluman kididdigar samarwa da rarraba wutar lantarki da hukumar ta fitar na baya bayan nan, hukumar kididdiga ta kasar ta nuna cewa, kasar ta Botswana ta samar da karfin megawatt 893,831 a rubu'i na 3 na shekarar 2017, inda ta karu da kashi 32.4 bisa 100, wato daga karfin megawatt 675,047 da ta samar a rubu'i na 2 na shekarar ta 2017.

Tashar lantarki ta Morupule B, mai nisan kilomita 270 a arewacin Gaborone, babban birnin kasar, ita ce ke samar da kashi 90 bisa 100 na adadin lantarkin da kasar ke amfani da ita a cikin gida.

An fara aikin samar da lantarki a kasar ta Botswana ne a shekarar 1985, da tashar samar da lantarki dake Morupule, wadda ke samar da karfin megawatt 132. Kafin wancan lokacin, an shigo da mafi yawan lantarkin da Botswana ke amfani da shi daga tashar samar da lantarki ta Eskom dake kasar Afrika ta kudu.

A shekarar 2008, bukatar lantarkin ta kasar Afrika ta kudu ta yi matukar karuwa, lamarin da ya sa ta rage fitar da lantarkinta zuwa kasashen ketare.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China