in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yaba da sahihin zabe a Liberia
2017-12-28 09:40:53 cri

Babban magatakardar MDD Antonio Guterres, ya jinjinawa masu ruwa da tsaki a babban zaben kasar Liberia, bisa kwazon su na gudanar da sahihin zabe cikin lumana.

Da yake bayyana hakan cikin wata sanarwa ta hannun kakakin sa Stephane Dujarric, Mr. Guterres, ya ce za a tura tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo, domin ya kasance mai baiwa Liberia goyon baya, a wannan gaba da kasar ke sauyin gwamnati karon farko cikin sama da shekaru 70 da kafuwar ta.

Mr. Guterres ya yi fatan zaben zai samu amincewar al'ummar kasar ta Liberia, ya kuma share fagen sauyin gwamnati bisa doka kuma ciki lokacin da kundin mulkin kasar ya tanada. Al'ummar Liberia dai sun kada kuri'un su a zagaye na biyu ne a ranar Talata.

Tsohon mataimakin shugaban kasar Joseph Boakai, da kuma tsohon tauraron kwallon kafar kasar George Weah ne suka fafatawa a wannan zagayen. Kafin hakan an gudanar da zagayen farko cikin watan Oktoba. Kana aka sanya lokacin gudanar zagaye na 2 na zaben a watan Nuwamba, kafin kuma a daga lokacin, bisa zargin da dan takara na 3 ya yi na saba wasu ka'idojin zabe.

Cikin wani jawabi da ta gabatar a zauren MDD a watan Satumbar da ya gabata, shugabar Liberia mai barin gado Ellen Johnson Sirleaf, wadda kuma ita ce mace daya tilo da ta taba shugabantar wata kasa a nahiyar Afirka, ta ce ana sa ran babban zaben kasar na bana, zai dora Liberia bisa turbar dimokaradiyya mai nagarta.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China