Shugaba Xi Jinping, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin koli na JKS, shi ne ya jagoranci taron sashen siyasar na ranar Larabar nan, taron da kuma mahalartansa suka saurari rahoton aiki, daga kwamitin ladaftarwa da sanya ido na kwamitin kolin, tare da tattaunawa game da alkiblar da jam'iyyar ta sanya gaba, game da yaki da cin hanci da rashawa a shekarar ta 2018 mai zuwa. (Saminu Hassan)