in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen Afirka na maimaita fasahar neman ci gaba da kasar Sin ta samu
2017-12-26 11:02:08 cri

Jama'a masu sauraro, yanzu a nahiyar Afirka wadda ke da nisa sosai daga nan kasar Sin, ana iya ganin Sinawa a kullum, mai yiwuwa ne su masu yawon bude ido ne, ko 'yan kasuwa, ko hafsoshi ko sojoji masu tabbatar da zaman lafiya a Afirka, har ma da masu aikin jinya ko wadanda suke aiki a kamfanoni masu jarin kasar Sin.

A duk inda suke da zama ko yin aiki, dukkansu suna kokarin aiwatar da manufar sada zumunci da sahihanci a tsakanin Sin da Afirka. Yanzu ga wani rahoton da abokin aikinmu Sanusi Chen ya hada mana.

A lokacin da kasar Sin take taka muhimmiyar rawa a duk duniya, duk wanda yake zaune a Afirka yana kuma sada zumunci ga jama'ar Afirka, domin samar da karfin kasar Sin ga ci gaban Afirka, da cimma burin farfadowar Afirka. Alal misali, a lokacin da kasashen Afirka ke tinkarar cututtuka da bala'i daga indallahi, tabbas kasar Sin ta baiwa kasashen Afirka taimako.

A ran 26 ga watan Nuwamba, a kasar Tanzaniya dake gabashin Afirka, jirgin ruwan Peace Ark na rundunar sojin ruwan kasar Sin dake kula da aikin jinya ya kammala ziyararsa ta farko, ta kewayen nahiyar Afirka ya tashi daga tashar ruwa ta Dares Salam. A cikin kwanaki kusan dari, jirgin ya yi tafiya fiye da mil dubu 13, ya ziyarci kasashen Djibouti da Saliyo da Gabon da Congo Brazaville da Angola da Mozambique da Tanzania, inda ya samar da aikin jinya ga marasa lafiya dubu 52 na wadannan kasashe, har ma aka yi aikin tiyata sau 246 a jirgin. A idon al'ummomin kasashen Afirka, wannan jirgin Peace Ark yana ba su fatan alheri da kuma sada zumunci.

A watan Agusta, bala'in ambaliyar ruwa da zaftarewar laka ya haddasa mutuwar mutane fiye da dubu 1 sakamakon ruwan sama da aka sha a birnin Freetown na kasar Saliyo. Bayan aukuwar bala'in, rukunin ceto da kamfanonin kasar Sin dake kasar Saliyo suka tura ya zama rukunin ceto na farko da kasashen waje suka tura. Sannan ba tare da bata lokaci ba, kwararru likitocin soja na kasar Sin dake aiki a kasar Saliyo sun ba da amsa cikin sauri, sun ba da aikin jinya da kuma daukar matakan hana yada annobar cututtuka.

Bugu da kari, kasar Sin tana kokarin daukar matakai iri iri wajen tabbatar da zaman lafiya a kasashen Afirka.

A ran 1 ga watan Agusta, rundunar sojan ba da tabbaci na kasar Sin ta shiga sansaninsa da aka kafa a Djibouti, wannan ne sansanin ba da tabbaci na farko da kasar Sin ta gina a ketare. Bisa wannan sansani, sojojin kasar Sin za su iya kare jiragen ruwan jama' a da kuma aikin agaji a yankin teku na Aden da na Somaliya kamar yadda ake fata.

Sannan a kasar Sudan ta kudu, ko a kasar Mali, ko a kasar Congo Kinshasa, sojojin kasar Sin masu sanya "hular launin shudi" sun zama mutanen da suka fi samun karbuwa. A lokacin da suke sauke nauyin tabbatar da zaman lafiya a wadannan kasashe da MDD ta dora musu, su kan yi kokarin taimakawa al'ummomin wurin wajen kawar da wahalolin da suke sha.

Sannan kuma, kasar Sin ba ta boye fasahar neman ci gaba da ta samu ba, a lokacin da take taimakawa kasashen Afirka wajen neman bunkasa tattalin arzikinsu.

A karshen watan Mayun da ya gabata, an kaddamar da layin dogo dake hade Nairobi, fadar mulkin kasar Kenya da birnin Mombasa, wata tashar ruwa dake gabashin kasar. Wani kamfanin kasar Sin ne ya shimfida wannan layin dogo bisa ma'aunin kasar Sin. Bayan da aka kaddamar da shi zuwa yanzu, adadin fasinjojin da aka yi jigilar su ta wannan layin dogo ya kai fiye da dubu dari 6.

A ran 2 ga watan Nuwamba, an kuma kaddamar da dam na Soubre mai samar da wutar lantaki dake kan kogin Sassandra na kasar Kwadifwa. Wannan aiki ne da ke alamta yadda kasar Sin da kasashen Afirka suke hadin gwiwa wajen samar da kayayyakin more rayuwar jama'a. Ba ma kawai wannan aiki yana samar da karin wutar lantaki ba, har ma yana samar da dimbin guraban aikin yi.

A taron koli na kungiyar AU karo na 29 da aka shirya a watan Yuli, madam Amina Mohamed, mataimakiyar babban sakataren MDD dindindin ta ambaci shawarar "hanya daya da ziri daya" da kasar Sin ta gabatar, inda ta nemi kasashen Afirka da su yi amfani da wannan damar da ba a taba ganinta a tarihi ba, domin cimma burin bunkasa nahiyar Afirka gu daya.

Yanzu a nahiyar Afirka, kasar Habasha ta zama wani abin koyi ga sauran kasashen Afirka wajen neman samun ci gaban tattalin arziki. A kan yi sharhi cewa, tana samun ci gaba kamar yadda kasar Sin ta taba samu. Bugu da kari, kasashen Rwanda da Kenya da Uganda da kuma Angola da dai sauransu su ma suna sa idanunsu kan kasar Sin, suna nazarta da kuma koyon "hanyar da kasar Sin take bi". Yanzu haka suna kan gaba a duk fadin Afirka wajen bunkasa tattalin arzikinsu. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China