in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An saki jami'ai da 'yayan masarautar Saudiyya su 20 bayan sun amsa laifin aikata rashawa
2017-12-26 10:59:15 cri

Kimanin jami'an kasar Saudiyya da 'yayan masarautar kasar su 20 ne aka sake su bayan da bayanai suka fito cewa, sun amsa laifin da ake tuhumar su da shi na aikata rashawa, kafafen yada labaran kasar ne suka fitar da rahoton a jiya Litinin.

Ana sa ran sakin karin wasu mutanen nan ba da jimawa ba a matsayin wani mataki na cika alkawarin da gwamnatin Saudiyyan ta dauka na kawo karshen ayyukan rashawa mafi girma a tarihin kasar wanda ya yi matukar daukar hankalin duniya.

A farkon wannan watan ne hukumomin kasar Saudiyya suka sanar a hukumance cewa, sun garkame mutane 159 da ake zargin su da hannu wajen aikata rashawa. Kuma mafi yawan wadanda ake zargin sun amsa laifukan aikata rashawar.

Tun a watan jiya ne dai, kafafen yada labaran Saudiyya suka rawaito cewa, 'yan gidan sarautar kasar 11 da kuma wasu tsoffin ministocin kasar da wadanda suke kan mulki 38 ne ake tsare da su bisa zargin su da hannu wajen aikata rashawa.

Sarki Salman bin Abdulaziz Al Saud na kasar, da yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman ne suka ba da umarnin kama jami'an.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China