in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Turkiyya ta kori wasu karin jami'ai 2,700 daga aiki
2017-12-25 12:23:54 cri
Mahukuntan kasar Turkiyya, sun sallami karin jami'an tsaron kasar sama da 2,700 daga bakin aiki, bisa laifin samun su da hannu a yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba da aka yi a bara.

Wata sanarwar gwamnatin kasar ta bayyana cewa, jami'an sun kunshi ko dai 'yan kungiyoyin ta'adda, ko kuma mambobin kungiyoyin dake yiwa tsaron kasar kafar ungulu. An kuma kore su daga aikin ne bisa tanajin wata doka ta soja. A hannu guda kuma, an maida wasu jami'ai su 115 bakin aikin su, bayan korar da aka yi musu a baya.

Mahukuntan Turkiyyar dai na ci gaba da gudanar da bincike, tare da daukar matakan hukunta wadanda aka samu da hannu a yunkurin juyin mulkin soji da bai yi nasara ba na watan Yulin da ya gabata. Lamarin da kuma ya sabbaba kisan mutane 250.

Kawo yanzu dai an kori ko dakatar da jami'ai sama da 150,000 daga aiki, kana ana tsare da wasu 55,000, bisa batun juyin mulkin da mahukuntan Turkiyyan ke alakantawa da malamin addinin nan Fethullah Gulen, wanda yanzu haka ke gudun hijira a Amurka.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China