in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ba wanda ya samu moriya daga batun ficewar Birtaniya daga EU
2017-12-25 11:05:10 cri

A shekarar 2017 dake daf da karewa, ana ci gaba da gudanar da shawarwarin game da batun ficewar Birtaniya daga kungiyar tarayyar kasashen Turai EU a birnin Brussels, batun da ake ganin cewa, ba zai haifar da moriya ga sassan dake da ruwa da tsaki a cikin sa ba.

A yammacin ranar 29 ga watan Maris na shekarar nan ta bana ne a birnin Brussels na kasar Belgium, shugaban majalisar kasashen Turai ya yi hanzarin shiga dakin watsa labarai, na sabon ginin majalisar kasashen Turai EU tare da wata wasikar da jakadan kasar Birtaniya dake EU ya mika masa a madadin firayin ministar kasar Theresa May, inda ya bayyana cewa, ga ta nan, sanarwar ficewa daga EU ce da firayin minisar Theresa May ta gabatar, abin bakin ciki ne da ake fuskanta.

Daga nan aka fara gudanar da shawarwari kan batun, sassan biyu wato EU da Birtaniya suna kokari matuka domin kammala shawarwarin cikin shekaru biyu bisa tanajin doka, wato kafin ranar 29 ga watan Maris na shekarar 2019. A ranar 29 ga watan Afililun bana, kungiyar tarayyar kasashen Turai ta shirya taron koli na musamman, inda shugabannin kasashe mambobin EU ban da Birtaniya, suka zartas da manufar ba da jagoranci kan shawarwarin, wato suka tsai da kuduri cewa, za su yi shawarwari da Birtaniya kan batun bisa matakai daban daban.

Bayan da aka kammala babban zabe a Birtaniya, sai aka fara gudanar da shawarwari kan batun ficewar kasar daga EU a hukumance a ranar 19 ga watan Yunin bana. Babban wakilin EU kan batun Michel Barnier da ministan Birtaniya mai kula da batun David Davis sun yi shawarwari tsakanin tawagogin dake karkashin jagorancinsu sau daya a kowane wata, amma har zuwa ranar 10 ga watan Nuwamban bana, wato bayan shawarwari karo na 6 da suka yi, sassan biyu ba su cimma ra'ayi daya kan batutuwa uku da suka fi jawo hankalinsu ba tukuna; wato yadda za a tabbatar da hakkin 'yan asalin kasashen mambobin EU miliyan uku dake zaune a Birtaniya, da 'yan asalin kasar Birtaniya miliyan daya dake zaune a sauran kasashen mambobin EU, da adadin kudin da Birtaniya za ta biyawa EU domin cimma burin ficewa daga kungiyar, da iyakar kasar dake tsakanin Ireland da Birtaniya.

A sanadin haka, a ranar 24 ga watan Nuwamban bana, shugaban majalisar kasashen Turai, ya bukaci Theresa May da ta tabbatar da amsarta kan adadin kudin da kasarta za ta biya domin ficewa daga EU a cikin kwanaki goma. Ya zuwa ranar 4 ga wannan wata, Theresa May ta je Brussels domin tattaunawa da wakilan da abin ya shafa, amma ba su samu sakamako ba, inda May ta bayyana cewa, "Mun cimma ra'ayi daya kan batutuwa da dama, kana abu mafi muhimmanci shi ne muna fatan za mu samu ci gaba tare, amma abu mai faranta ran mutane shi ne, mun fara warware wasu sabani dake tsakaninmu, shi ya sa ya fi dacewa mu ci gaba da yin shawarwari."

Daga baya wato ya zuwa ranar 8 ga wata, May ta sake zuwa hedkwatar EU. Shugaban kwamitin EU Jean Claude Juncker ya amince da sakamakon da sassan biyu suka samu bisa mataki na farko, Juncker ya ce, "Mun tattauna kan rahoton da wakilan shawarwarin suka gabatar, firayin ministar May ta tabbatar da cewa, rahoton ya riga ya samu amincewa daga wajen gwamnatin Birtaniya, muna ganin cewa, mun riga mun samu sakamakon da muke bukata. Duk da cewa, akwai matsala dake gabanmu yayin da muke gudanar da shawarwarin."

Bisa shirin da EU ta tsara, sassan biyu za su fara yin shawarwari bisa mataki na biyu, inda za a tattauna kan batun game da lokacin wucin gadi na aikin ficewar Birtaniya daga EU.

Game da huldar dake tsakanin EU da Birtaniya a nan gaba, sau da dama EU ta bayyana cewa, tana fatan raya hadin gwiwar dake tsakaninta da Birtaniya a fannonin tattalin arziki, da ciniki, da yaki da ta'addanci, da laifuffukan kasa da kasa, da tsaron kasa, da harkokin diplomasiyya da sauransu.

Daraktan zartaswa na cibiyar Asiya da Turai Fraser Cameron yana ganin cewa, ba ma kawai shawarwarin ficewar Birtaniya daga EU yana da sarkakiya ba, har ma kudurin Birtaniya na ficewa daga EU ba shi da hankali, ya ce, "Ko shakka babu kudurin yana tattare da matsaloli, duba da cewa EU da ita kan ta Birtaniya, ba za ta samu wata moriya daga gare shi ba, musamman ma ita Birtaniya, batu ne da zai haifar mata da babbar illa."(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China