in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Isra'ila za ta fita daga UNESCO
2017-12-25 10:52:54 cri

Wasu rahotanni na cewa kasar Isra'ila za ta fice daga hukumar kyautata ilmi, kimiyya da al'ada ta MDD wato UNESCO a karshen shekarar bana.

A ranar 22 ga wata, firaministan kasar Benjamin Netanyahu ya ba da umurni ga wakilin kasar dake hukumar, da ya bar hukumar kafin ranar 31 ga watan nan da muke ciki a hukunce.

Haka kuma, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Isra'ila ya bayyana cewa, an tsai da wannan kuduri ne domin hukumar UNESCO "tana da nufin raba tarihin Yahudawa daga kasar ta Isra'ila".

Bugu da kari, wani babban jami'in gwamnatin Isra'ila ya nuna cewa, idan hukumar UNESCO ta yi kwaskwarima, da kuma daidaita matsayinta kan harkokin Isra'ila kafin karshen shekarar 2018, kasarsa za ta soke wannan kuduri. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China