in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta jadadda goyon bayanta ga 'yancin kan Falasdinu
2017-12-23 13:02:30 cri
Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya ce kasar Sin na goyon bayan kafa kasashe biyu da kuma 'yancin kan Falasdinu, wanda ke da cikakken iko bisa iyakar da aka shata a shekarar 1967 da kuma kasancewar gabashin birnin Kudus a matsayin babban birninsa.

Wang Yi ya bayyana haka ne a jiya, lokacin da yake ganawa da Ahmed Majdalani da Nabil Shaath wadanda suka zo kasar Sin a matsayin wakilan shugaban Falasdinu.

A ranar Alhamis da ta gabata ne babban zauren MDD, ya amince da wani kuduri da ya yi watsi da duk wani mataki da zai sauya matsayin birnin Kudus.

A cewar wang Yi, matakin babban zauren ba kadai nuna matsayar al'ummar kasashen waje ya yi ba, har ma da yin kira da a gaggauta tabbatar da zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya.

Ya kuma yi kira da bangaren Falasdinu, ya kafa wata hadaddiyar tawaga, da za ta dage wajen warware rikice-rikice da fadada rawar da MDD ke takawa da kuma kausasa kiran neman zaman lafiya.

A nasu bangaren, Ahmed Majdalani da Nabil Shaath, sun bayyana godiyarsu ga goyon bayan da kasar Sin ke ba muradin al'ummar Falasdinu, suna masu fatan kasar Sin za ta kara taka rawar gani game da batun yankin gabas ta tsakiya. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China