in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rundunonin tsaron Nijeriya na zaune cikin shiri gabanin bukukuwan karshen shekara
2017-12-23 12:46:17 cri
Shugabannin rundunonin tsaron Nijeriya, sun sanya dukkan jami'ansu zama cikin shiri don tunkarar duk wani yanayin gaggawa da ka iya aukuwa yayin bukukuwan karshen shekara.

Rundunar sojin Nijeriya ta yi kira ga mutanen dake zaune a yankin arewa maso gabashin kasar dake fama da rikicin ta'addanci, su yi taka tsantsa tare da tsare kawunansu daga harin kunar bakin wake daga kungiyar Boko Haram.

Kakakin rundunar Col. Onyema Nwachukwu, ya ce abu ne mai muhimmanci, jama'a su yi taka tsantsa tare da lura da mutanen da ba su yadda da su ba a cikin al'ummominsu da wuraren ibada da sauran wuraren taron jama'a

Ya kuma yi kira da shugabannin addini da na al'umma, su wayar da kan jama'arsu game da matakan tsaro don kare aukuwar harin 'yan ta'adda.

Haka zalika, rundunar 'yan sandan jihar Kano dake arewa maso yammacin kasar, ta tabbatarwa al'ummar jihar cewa an dauki matakan da suka dace na tabbatar da tsaro yayin bukukuwan kirismeti da na karshen shekara. An kuma tura jami'ai wuraren ibada da tasoshin mota da kasuwanni da tituna da manyan shaguna da wuraren shakatawa da sauran wuraren taron jama'a domin tabbatar da tsaro.

Ita ma rundunar 'yan sandan Jihar Adamawa dake arewa maso gabashin kasar, ta ce ta dauki matakan tsaro domin tabbatar da gudanar bukukuwan lami lafiya.

A Jihar Akwa Ibom mai arzikin man fetur kuwa, an baza jami'an 'yan sanda 6,000 domin samar da tsaro yayin da kuma bayan bukukuwan. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China