in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Gambia sun sha alwashin karfafa hadin gwiwa
2017-12-22 21:15:26 cri
Mahukuntan kasashen Sin da Gambia sun sha alwashin karfafa hadin gwiwa da juna, a fannin raya fasahohin aikin gona, da sarrafa kifi, da gina ababen more rayuwa, da yawon bude ido, a wani mataki na cimma moriyar juna tsakanin kasashen biyu.

Da yake tabbatar da hakan a Juma'ar nan, yayin ganawar sa da shugaban kasar Gambia Adama Barrow, firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya ce Sin za ta ci gaba da samar da dukkanin tallafin da ya dace, domin farfado da tattalin arzikin Gambia, da ma zamantakewar al'ummar kasar.

Firaministan na Sin ya kara da cewa, kasar sa na fatan Gambia za ta ci gaba da riko da kudurin nan na kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, yayin da Sin din ke fatan tabbatar da ci gaban Gambia bisa mutunta juna, da martabawa.

Da yake maida jawabi, shugaba Barrow ya ce kasar sa na fatan ci gaba da samun taimako daga Sin a nan gaba. Ya kuma alkawarta aniyar kasar sa ta ci gaba da martaba kudurin wanzuwar kasar Sin daya tak a duniya.

Ya ce Gambia za ta hada kai da Sin, wajen bunkasa hadin gwiwar dake tsakanin su, ta yadda za a kai ga daga matsayin alakar sassan biyu zuwa wani sabon mataki.

Shi ma dan majalissar wakilan jama'ar kasar Sin Zhang Dejiang ya gana da Mr. Barrow a Juma'ar nan.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China