in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sama da mutane miliyan 40 ne ke fama da yunwa a yankin NENA
2017-12-22 11:06:09 cri
Hukumar samar da abinci da kula da harkokin gona ta duniya FAO, ta ce mutane sama da miliyan 40 ne ke fama da yunwa a yankin NENA da ya kunshin yankunan arewacin Afrika da na kusa da gabashin duniya, saboda yake-yake da rikice-rikice.

Wani sabon rahoton hukumar da aka fitar jiya Alhamis, ya ce mutane miliyan 40. 2 ne ke fama da rashin sinadaran gina jiki da yunwa, yayin da wasu miliyan 55.2 ke fama da matsananciyar yunwa saboda rikicin yankin.

Galibin kasashen NENA, sun hada da na yankin gabas ta tsakiya da na Larabawa, ciki har da Masar da Syria da Iraqi da Yemen da Libya da Sudan da Saudiyya da dai sauransu.

Rahoton na FAO ya ruwaito cewa tsakanin shekakarar 2014 zuwa 2016, kaso 27.2 na mutanen kasashen yankin da yaki ya daidaita na fama da matsananciyar yunwa ko kuma rashin sinadaran gina jiki, yana mai bayyana kasashen Syria da Iraqi da Yemen da Libya a matsayin inda matsalar ta fi kamari.

Hukumar ta bayyana zaman lafiya a yankin a matsayin hanya daya tilo, ta kawo karshen yunwa kawo shekarar 2030, kamar yadda yake kunshe cikin muradun ci gaba masu dorewa da kasashen duniya suka amince da su. (Fa'iza Msuatpha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China