in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanonin Sin sun je jami'ar Nairobi don hayar ma'aikata
2017-12-22 10:39:31 cri

A ranar 20 ga wata, kwalejin koyar da Sinanci ta Confucius da aka kafa a jami'ar Nairobin kasar Kenya da kungiyar tattalin arziki da ciniki dake tsakanin kasaashen Sin da Kenya da babbar kungiyar kasuwancin kasar Sin dake kasar Kenya sun shirya wani taron daukar hayar ma'aikata a jami'ar ta hanyar hadin gwiwa, inda kamfanonin kasar Sin sama da 40 suka halarci taron domin daukar hayar ma'aikata kusan 1000.

A shekarar da ta gabata, kwalejin koyar da Sinanci ta Confucius da aka kafa a jami'ar Nairobin kasar Kenya ta taba shirya irin wannan taron daukar hayar ma'aikata a jami'ar, taron da ya samu karbuwa matuka daga wajen daliban da zasu kammala karatu a jami'ar, har sama da dari daya sun samu guraben aikin yi a kamfanonin kasar Sin dake kasar ta Kenya. Yanzu haka bukatun hayar ma'aikata na kamfanonin kasar Sin suna karuwa sannu a hankali, a saboda haka adadin kamfanonin da suka halarci taron da yawan ma'aikatan da za su yi hayar su suma sun karu zuwa babban mataki.

Shugabar kwalejin koyar da Sinanci ta Confucius da aka kafa a jami'ar Nairobin kasar Kenya da gwamnatin kasar Sin ta nada Guo Hong, ta bayyana cewa, "Mun lura cewa, yawancin daliban da suka kammala karatu a jami'ar sun kasa samun guraben aikin yi cikin lokaci, sai hutu suke yi gida, dalilin da yasa haka shine domin basu samu damar yin cudanya da kamfanonin dake hayar ma'aikata ba, shi yasa mun shirya taron domin samar da taimako gare su, tare kuma da samar da dama ga kamfanonin wadanda ke bukatar hayar ma'aikata."

A baya daliban da suka kammala karatu a jami'o'i a kasar Kenyan sukan nemi guraben aikin yi ne ta hanyar duba tallar da aka buga a jaridu ko kuma ta yanar gizo, yanzu kuma taron yin hayar ma'aikatan da aka shirya ya bai wa daliban mamaki matuka.

Susan Gitau, shugabar kwalejin koyar da fasahohin sana'o'i ta Afirka ta zo jami'ar Nairobi ne daga garin Thika dake da nisan kilomita 40 daga birnin Nairobin tare da dalibai sama da 50 domin neman samun guraben aikin yi da suke bukata, Susan tana ganin cewa, ya kamata a kara gudanar da irin wannan taron a sauran wuraren fadin kasar, ta ce, "A baya daliban da suka kammala karatu a jami'a su kan je kamfanoni da kansu domin neman guraben aikin yi, kuma da dama daga cikinsu basu san ina ne za su je ba, yanzu dai an shirya wannan taro, daliban suna iya yin cudanya da kamfanoni da dama a cikin yini guda daya kacal, ko shakka babu dama ce mai kyau gare su, ina fatan hukumomin da abin ya shafa na gwamnatin kasar Kenya da kamfanonin kasar zasu koyi wannan hanyar samar da guraben aikin yi, kuma zasu shirya irin wannan taro a nan gaba."

Dennis Obiero, dalibi ne dake karatun sana'ar injiniya a jami'ar Kenyatta, ya zo wurin taron tare da abokan karatunsa su biyar, tun lokacin da aka kaddamar da taron a wannan rana, kuma ya nuna sha'awa matuka kan aikin injiniya a fannonin gina gine-gine, ya gaya mana cewa, "Kamfanonin kasar Sin sun zo kasarmu ta Kenya ne tare da fasahohi na zamani, shi ya sa idan na samu damar yin aiki tare da kwararrun kasar Sin, to ko shakka babu zan koyi fasahohi da dama da nake bukata, har zasu taimaka mana domin mu gudanar da aiki a manyan kamfanoni a nan gaba, muna farin ciki sosai da ganin kamfanonin kasar Sin da suka zo jami'ar don samar da guraben aikin yi, kuma a fili ne suke gudanar da aikin yin haya bisa adalci, muna iya samun aikin yi bisa kwarewarmu."

Bisa alkaluman da aka samar, an ce, a cikin 'yan shekarun da suka gabata, daga daya cikin kamfanonin kasar Sin dake gudanar da aiki a kasar Kenya kusan 400 sun riga sun samar da guraben aikin yi wajen dubu 120 ga al'ummun kasar ta Kenya.

Mukadashin jakadan kasar Sin dake Kenya Li Xuhang, ya gabatar da wani jawabi a yayin taron daukar hayar ma'aikatan, inda ya bayyana cewa, yana fatan matasan kasar Kenya zasu sanya kokari tare da kamfanonin kasar Sin domin samar da makoma mai haske a kasar, ya ce, "Kasar Sin tana kara karfafa hadin gwiwar dake tsakaninta da sauran kasashen duniya, kuma ta gabatar da shawarar ziri daya da hanya daya, ana iya cewa, hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Kenya ya shiga wani sabon mataki, a nan kuma ina fatan kamfanonin kasar Sin zasu samar da damammaki ga matasan Kenya domin su amfanawa juna tare kuma da samun ci gaba yadda ya kamata."

Shugaban jami'ar Nairobi Peter Mbitihi shi ma ya gabatar da wani jawabi a yayin taron, inda ya nuna fatan alherinsa ga daliban dake neman samun aikin yi, tare kuma da nuna godiya ga kamfanonin kasar Sin wadanda ke samar da guraben aikin yi ga matasan kasar.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China