in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya gana da takwaransa na Gambia
2017-12-21 21:13:32 cri
A yau Alhamis, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na kasar Gambia Adama Barrow wanda a halin yanzu ke ziyarar aiki a nan kasar ta Sin, inda suka amince da kara bunkasa hadin gwiwa da mu'amala a tsakanin kasashen biyu.

A yayin ganawar, shugaba Xi Jinping ya yi nuni da cewa, a watan Maris na bara, an farfado da huldar diplomasiyya a tsakanin Sin da Gambia, matakin da ya bude wani sabon babi na huldar kasashen biyu. Ya ce alal hakika, wannan shawara da Gambia ta yanke ta dace da moriyar al'ummar kasashen biyu, kuma zabi ne da yayi daidai.

Shugaba Xi ya kara da cewa, Sin da kasashen Afirka aminan juna ne, kuma 'yan uwan juna. Kaza lika Gambia kuma mamba ce sabuwa a dandalin tattaunar hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka.

Shugaba Xi ya kara da cewa, Sin tana son hada kai da Gambia wajen tabbatar da sakamakon da aka cimma a gun taron kolin dandalin da aka gudanar a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu, don amfanar al'ummun kasashen biyu.

A nasa bangaren Shugaba Barrow ya ce maido da huldar diplomasiyya a tsakanin kasashen biyu, buri ne na al'ummar kasar Gambia, kuma kasar tana son nacewa ga bin manufar kasar Sin daya tak a duniya. Har ila yau Sin sahihiyar kawa ce ta kasashen Afirka, kuma Gambia tana fatan ci gaba da kokarin hada hannu da kasar Sin, a karkashin tsarin dandalin tattaunawar hadin gwiwa a tsakanin Sin da kasashen Afirka. (Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China