in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An shirya taron raya tattalin arzikin kasar Sin a Beijing
2017-12-21 10:50:13 cri

Kwamitin koli na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, ya shirya wani taron raya tattalin arzikin tsakanin ranakun 18 zuwa 20 ga wata a nan birnin Beijing, inda shugaban kasar Xi Jinping ya yi bayani kan yanayin da tattalin arzikin kasar ke ciki a halin yanzu, tare kuma da fitar da wasu manufofi domin ba da jagoranci kan aikin raya tattalin arziki a shekarar 2018 dake tafe.

A yayin taron hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da aka gudanar a ranar 8 ga wata, an fitar da wasu manufofin raya tattalin arzikin kasar a shekarar 2018 mai zuwa, inda aka jaddada cewa, kasar Sin za ta kara mai da hankali kan ingancin karuwar tattalin arziki, haka kuma za ta himmatu wajen tsarin tattalin arziki da ke samar da kayayyaki kwaskwarimar ta yadda zai kai ga habakar kasuwanni da kuma bude kofa ga kasashen waje daga duk fannoni.

Masani tattalin arziki dake aiki a cibiyar cudanyar tattalin arziki tsakanin kasa da kasa ta kasar Sin Zhang Yansheng ya bayyana cewa, taron raya tattalin arzikin da aka kira ya sake jaddada cewa, kasar Sin za ta himmantu kan aikin raya tattalin arziki mai inganci sannu a hankali bisa matakai daban daban, ya ce, "Ko a fannin yin kwaskwarima ga tsarin tattalin arziki wajen samar da kayayyaki, ko kuma a fannin kara kokarin raya tattalin arziki bisa sabon tsarin yau da kullum na kasar a sabon zamanin da muke ciki, ko shakka babu ya zama wajibi a mai da hankali kan aikin raya tattalin arziki mai inganci sannu a hankali, wato cikin kwanciyar hankali, kana abu mafi muhimmanci shi ne a yi kokarin magance hadarin kudi yayin da ake raya tattalin arzikin kasar."

Game da batun da aka tattauna yayin taron, wato yin kwaskwarima kan tsarin tattalin arziki a fannin samar da kayayyaki, Zhang Yansheng yana ganin cewa, manufofin da aka fitar a yayin taron suna da muhimmanci matuka ga ci gaban tattalin arzikin kasar a nan gaba, ya ce, "A yayin taron da aka gudanar, an tattauna sosai kan batutuwan da shugaba Xi Jinping ya sha jaddadawa, misali za a mai da hankali kan kirkire kirkire a maimakon kera kayayyaki kawai, kana za a mai da hankali kan inganci a maimakon sauri, ban da haka kuma za a mai da hankali kan ingancin kayayyakin da ake samarwa a maimakon yawansu, duk wadannan za su taka rawar gani kan aikin ci gaban tattalin arziki a kasar ta Sin a shekara mai zuwa."

Domin cimma burin raya tattalin arziki mai inganci, taron ya fitar da wasu hakikanan matakai, misali, kara zurfafa gyaran fuska kan kasuwanni, da sa kaimi kan ci gaban kamfanonin gwamnati, da nuna goyon baya ga ci gaban kamfanoni masu zaman kansu, da kara kyautata huldar dake tsakanin hukumomin gwamnati da 'yan kasuwa, da aiwatar da manyan tsare-tsare domin farfado da tattalin arzikin kauyuka, da bullo da manufofin warware matsalolin da al'ummun kasar ke fuskanta da sauransu.

Mataimakin darektan cibiyar nazarin manufofin raya kasa ta majalisar gudanarwar kasar Sin Wang Yiming ya bayyana cewa, manufofin da aka fitar a yayin taron sun nuna cewa, gwamnati ta fi mai da hankali kan muhimman muradun al'ummun kasar, ya ce, "Har kullum jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta fi mai da hankali kan muhimman muradun al'ummar kasar, bangarorin da suka shafi zaman rayuwar al'ummun kasar kamar ba da ilmi da kiwon lafiya da samar da guraben aikin yi da samar da tabbaci ga zaman rayuwarsu, kamata ya yi gwamnatin kasar ta dauki matakan da suka dace. Domin biyan bukatun al'ummun kasar yadda ya kamata, gwamnati ta kara mai da hankali kan aikin samar musu da gidajen kwana, ban da haka kuma gwamnati ta kara himmatuwa a fannin yaki da talauci a kasar,inda ta yi alkawari cewa, za ta warware matsalar cikin shekaru uku masu zuwa."

Hakazalika, taron ya sake jaddada cewa, nan gaba kasar Sin za ta kara ba da muhimmanci kan aikin kirkire kirkire, Wang Yiming ya ce, "A cikin shekaru biyu da suka gabata, kasar Sin ta samu sakamako a bayyane a fannin yin kirkire kirkire, lamarin da ya jawo hankalin al'ummun kasashen duniya, ina ganin cewa, nan gaba kamata ya yi kasar Sin ta kara mai da hankali kan aikin samar da wata kasuwa mai inganci ga masu kafa kamfanoni domin su kara yin kirkire kirkire."

Wang Yiming ya kara da cewa, manufar da kasar Sin ke dauka wato neman samun ci gaban tattalin arziki mai inganci, ta nuna cewa, kasar Sin tana kokarin cimma burin samun dauwamammen ci gaba bisa adalci.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China