Kalaman Trump kan wannan batu na zuwa ne, bayan da jakadar Amurka a MDD Nikki Haley ta wallafa a shafinta na Twitter cewa, Amurka za ta tattara sunayen kasashen da suka soki matakin Amurka game da birnin Kududs a babban zauren MDD.
A ranar Litinin ne dai Amurkar ta hau kujerar naki kan kudurin MDD game da matsayin birnin Kudus, inda kasashe 14 mambobin kwamitin sulhu suka goyi bayan kudurin da kasar Masar ta gabatar, ban da Amurka.
A yau ne kuma babban zauren MDD zai yi wani taron gaggawa da ba safai yake yi ba domin tattauna matsayin birnin na Kudus, bayan da tun farko Amurka ta hau kujerer naki kan kudurin da kasar Masar ta gabatar,wanda ke bukatar Amurka ta janye batun ayyana birnin Kudus a matsayin hedkwatar kasar ta Isra'ila.(Ibrahim)