Shugaban na Gambia dai zai gudanar da ziyarar ta sa ne daga ranar Laraba zuwa Talatar makon gobe, bisa gayyatar shugaban kasar Sin Xi Jinping.
Sin da Gambia sun sake maida huldar diflomasiyya ne a watan Maris na shekarar 2016, bayan dakatar da hakan tsawon shekaru 21.
Shugaba Barrow, shi ne shugaban Gambia na farko da zai ziyarci kasar Sin, tun bayan da sassan biyu suka maido da dangantakar diflomasiyya.