in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta himmatu wajen bullo da sabon yanayin bude kofa ga kasashen waje a dukkan fannoni
2017-12-20 13:18:45 cri

 

A yayin taron hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin da aka gudanar a kwanakin baya, an yi nuni da cewa, ya kamata a kara mayar da hankali wajen bullo da sabon yanayin bude kofa ga kasashen waje a dukkan fannoni. Wane irin yanayin da za a samar, kuma ta yaya za a aiwatar da shirin bude kofar, duk wadannan sun jawo hankalin masanan Sin da kasashen waje sosai.

A matsayin kasar dake kan gaba wajen fitar da kayayyaki a duniya kuma kasa ta biyu mafi shigar da kayayyaki, kana kasar mai tasowa mafi jawo jari daga kasashen waje, manufofin bude kofa da kasar Sin ta gabatar sun jawo hankalin kasa da kasa sosai. Tun bayan da aka fara aiwatar da manufar bullo da sabon yanayin bude kofa, shirin ya jawo hankalin duniya sosai. Shugaban gudanarwa na hukumar nazari ta bankin Hengfeng Dong Ximiao ya bayyana cewa, bullo da sabon yanayin bude kofa a dukkan fannoni ya fi dora muhimmanci ne ga sabbin fannoni ko hanyoyi. Ya ce,

"Ya kamata a samu sabbin fannoni da hanyoyi yayin da ake kokarin bullo da sabon yanayin bude kofa a dukkan fannoni. Kamar Sin ta sanar da sassauta kayyade sha'anin hada-hadar kudi yayin bude kofa ga kasashen waje, da neman sabbin hanyoyin jawo jari daga kasashen waje don fadada shirin bude kofa, da kuma yin amfani da shawarar 'ziri daya da hanya daya' wajen kara bude kofa ga kasashen waje."

Yayin da ake sa kaimi ga bude kofa, wata sabuwar hanya da aka bullo da ita, ita ce kafa yankin ciniki cikin 'yanci na gwaji. Daya daga cikin manyan kamfanonin ba da hidima na kasashen waje da suka fara shiga kasuwar kasar Sin, kamfanin Ernst & Young ya fahimci wannan fanni sosai. Shugaban fannin haraji na kamfanin Titus Von dem Bongart ya bayyana cewa, bunkasuwar tattalin arzikin Sin, da yadda kasuwar kasar Sin ta sauya sun taimakawa kamfaninsa matuka. Ya bayyana cewa,

"A cikin shekarun baya baya nan, Sin ta kafa yankin yin ciniki cikin 'yanci, ta kuma sassauta wasu ka'idojin da suke kawo nakasu ga kasuwannin kasar. A halin yanzu, masu cin gajiyar hidimarmu suna iya shiga kasuwar kasar Sin cikin 'yanci, kana mu ma muna iya samar da hidima yadda ya kamata, hakazalika kuma, karin kamfanonin kasashen waje sun shiga kasuwar kasar Sin."

A halin yanzu, Sin ta kafa yankunan yin ciniki cikin 'yanci guda 11, a daya bangaren kuma, birnin Shanghai da wasu biranen kasar, suna son kara gina tasoshin jiragen ruwa na yin ciniki cikin 'yanci. Mataimakin shugaban hukumar kula da harkokin ilmi na ma'aikatar harkokin ciniki ta kasar Sin Zhang Jianping yana ganin cewa, tasoshin jiragen ruwa na yin ciniki cikin 'yanci za su kara taimakawa wajen bude kofa da saukaka yanayin cinikayya. Ya ce,

"Yanzu ba a gabatar da wasu manufofin haraji a yankin ciniki cikin 'yanci ba, watakila sai a nan gaba idan za a kafa tasoshin jiragen ruwa na yin ciniki cikin 'yanci kamar yadda tasoshin ruwa na Dubai da Singapore suka yi, za a kara mai da hankali ga haraji da zirga-zirgar mutane da fadada wurin yin ciniki da sauransu. Yanzu birnin Shanghai ya mika shirinsa a wannan fanni ga kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin, kana lardunan Guangdong da Zhejiang suna kokarin gabatar da nasu shirin, don haka kafa tasoshin jiragen ruwa na yin ciniki cikin 'yanci za su kasance muhimmin bangare wajen taimakawa shirin bude kofa ga kasashen waje."

Masana na ganin cewa, kamata ya yi kasar Sin ta yi amfani da shawarar "ziri daya da hanya daya" wajen baiwa kamfanonin kasashen waje iznin shiga kasuwannin kasar Sin, a wani mataki na kara bude kofa ga kasashen waje. Farfesa Wang Yiwei na kwalejin kula da dangantakar kasa da kasa ta jami'ar Renmin ta kasar Sin ya yi nuni da cewa, a sabon yanayin da ake ciki, manufofin bude kofa ga kasashen waje na kasar Sin, ba wai sun taimaka ga ci gaban kasar Sin kawai ba, har ma sun taimaka ga samun 'yancin yin magana a fadin duniya. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China