in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na samar da hidimar kudi mai inganci ga bangaren tattalin arziki dake samar da kayayyaki da hidima
2017-12-19 10:42:26 cri

Kwanakin baya ne, hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta kira wani taro, inda aka tsara wasu manufofin raya tattalin arzikin kasar Sin a shekarar 2018 dake tafe.

Yayin taron, an yi nuni da cewa, a shekara mai zuwa, gwamnatin kasar Sin za ta himmantu ga aikin magance duk wata matsala yayin da take kokarin samar da hidimar kudi ga bangaren tattalin arziki dake samar da kayayyaki da hidima, ana sa ran cewa, za a ci gaba da tattauna batun a yayin taron raya tattalin arziki na kwamitin tsakiya na jam'iyyar JKS da za a shirya.

Tun daga farkon shekarar bana da muke ciki, wayar da ake kera na'urorin zuwa sararin samaniya ta kamfanin Xinguangshen na birnin Huainan na lardin Anhui dake nan kasar Sin ta kara samun karbuwa a kasuwar kasar, amma idan ana son kera wayar, ya zama wajibi a zuba jari mai tarin yawa kan aikin yin nazari da kuma kera su, haka kuma ana bukatar tsawon lokaci, ban da wannan kuma, ana bukatar kudi da dama wajen sayen kayayyaki domin kera wayar, manajan kamfanin Li Yong ya gaya mana cewa, "Mu kan kulla kwangiloli ne tsakanin kamfanimnu da kamfanonin kera na'urorin zuwa sararin samaniya, a saboda haka muna bukatar kudade da dama yayin da muke aikin yin nazari da kuma sayen kayayyakin da muke bukata, wannan ya sa mu kan yi fama da karancin kudi."

A karkashin irin wannan yanayi, bankin bunkasa harkokin kasuwanci a kauyuka na Tongshang na birnin Huainan a lardin Anhui na kasar Sin ya gudanar da kirkire-kirkire yayin da yake kokarin samar da hidimar kudi ga kamfanin, wato ya samar da rancen kudin da yawansa ya kai yuan miliyan 5 ga kamfanin Xinguangshen bisa kwangilolin da kamfanin ya daddale da wasu kamfanonin kera na'urorin zuwa sararin samaniya, hakan ya warware matsalar karancin kudin da kamfanin ke fuskanta, lamarin da ya zama abin koyi ga bankunan kasar Sin wajen samar da hidimar kudi mai inganci ga bangaren tattalin arziki dake samar da kayayyaki da hidima.

Shugaban hukumar sa ido da kuma tafiyar da harkokin bankunan kasar Sin Guo Shuqing ya taba bayyana cewa, "Nan gaba kasar Sin za ta ci gaba da himmatuwa kan aikin sa kaimi ga bankunan kasar domin su samar da hidima mai inganci ga bangaren tattalin arziki dake samar da kayayyaki da hidima, musamman ma aikin samar da hidimar kudi ga kananan kamfanoni da kuma ayyukan yaki da kangin talauci da samar da kayayyakin more rayuwar jama'a da samar da gidajen kwana ga al'ummun kasar."

Yayin taron hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya na jam'iyyar JKS, an kuma yi nuni da cewa, za a kara mai da hankali kan aikin magance babban rikicin kudi, masani tattalin arziki dake aiki a cibiyar nazarin kudi ta jami'ar Renmin ta kasar Sin Dong Ximiao ya bayyana cewa, dalilin da ya sa haka shi ne domin yawancin kamfanonin kasar ba su saba tattara kudaden da suke bukata kai tsaye ba, idan ana son rage rikici a wannan fannin, ya kamata kamfanonin kasar Sin su kara tattara kudaden da suke bukata kai tsaye.

Kana domin magance aukuwar hadarin kudi daga duk fannoni a nan kasar Sin, gwamnatin kasar ta fitar da shirin sarrafa manufar kudi bisa manyan tsare-tsare, shugaban babban bankin jama'ar kasar Sin Zhou Xiaochuan ya bayyana cewa, "Babban Bankin jama'ar kasar Sin yana kokari matuka domin kyautata manufar kudin kasar, musamman ma bayan da aka gamu da matsalar kudi a fadin kasashen duniya, yanzu haka an dauki wasu sabbin matakai, kuma an yiwa wasu manufofin da ake aiwatarwa gyaran fuska, misali idan tattalin arziki ya samu ci gaba ba tare da wata matsala ba, to kasuwar hannun jari ita ma ta kan gudana yadda ya kamata, kamfanonin kasar su ma suna iya samun riba mai tsoka, amma idan aka gamu da matsala, watakila za a gamu da matsala, a saboda haka dole ne a dauki matakan magance matsalar kafin ta kunno kai."

Masani kan batun kasar Sin na asusun nazarin manufofin harkokin waje na kasar Girka Gorgos Tzogopoulos ya yaba matuka da matakan da kasar Sin ta dauka a wannan fannin, ya ce, "Kasar Sin tana kokarin aiwatar da harkokin kudi yadda ya kamata, haka kuma ta dauki matakai da suka dace, ana iya cewa, kasar Sin ta warware matsaloli da dama, ana kuma sa ran kasar Sin za ta ci gaba da kokari tare kuma da samun sakamako mai gamsarwa."(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China