in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ci gaban nahiyar Afirka a shekarar 2017
2017-12-18 10:25:51 cri

Cikin shekarar 2017, kasashen Afirka sun samu ci gaba na a zo a gani, musamman ma a bangarorin gina kayayyakin more rayuwa, da aikin sadarwa, da dai makamantansu.

Kamar yadda kungiyar tarayyar Afirka AU ta tsara cikin "Ajandar raya nahiyar nan da shekarar 2063", kasashen Afirka suna kokarin samun ci gaban al'ummunsu ta hanyar kara dunkulewar nahiyar waje guda, da kokarin daidaita tsarin tattalin arzikin nahiyar.

Asusun ba da lamuni na duniya (IMF) ya yi hasashen cewa, saurin karuwar tattalin arzikin kasashen dake kudu da hamadar Sahara ka iya kaiwa kashi 2.6% a shekarar 2017, wanda ya karu sosai, idan an kwatanta da kashi 1.4% da aka samu a shekarar 2016.

Cikin dalilan da suka haifar da wannan karuwa, akwai kokarin habakar kayayyakin more rayuwar jama'a a kasashen Afirka daban daban. Wani misali a wannan bangare shi ne, yadda aka fara yin amfani da layin dogo da ya hada Nairobi da Mombasa na kasar Kenya, wanda wani kamfanin kasar Sin ya dauki nauyin shimfida shi. Rahotanni na cewa, al'ummar kasar Kenya sun yaba da wannan layin dogon sosai, kan yadda yake haifar da alfanu ga tattalin arziki da al'ummomin kasar.

Haka zalika, a kasar Habasha, gwamnatin kasar ta sanar a watan da ya gabata cewa, bankin duniya ya baiwa kasar tallafin kudi da yawansa ya kai dalar Amurka miliyan 380 domin gina tashoshin samar da wutar lantarki. Ta wannan hanya, ana fatan kara samar da wutar lantarki cikin shekaru 7 masu zuwa, don taimakawa karin kauyuka samun makamashi mai tsabta.

Sai dai "Ajandar raya nahiyar nan da 2063" da kungiyar AU ta tsara ta kunshi wasu shirye-shiryen da suka shafi dinke kasashen Afirka a waje guda, da tabbatar da kwanciyar hankali da walwala a nahiyar, wadanda suke bukatar aiwatar da wasu gyare-gyare ta fuskoki daban daban.

Ta fuskar tattalin arziki, akwai bukatar raya masana'antu da sana'o'i iri-iri. A cewar Asusun ba da lamuni na duniya (IMF), dole ne kasashen Afirka su yi kokarin daidaita tsare-tsaren tattalin arzikinsu, da inganta kayayyakin more rayuwa, don samar da yanayin zuba jari mai kyau, sa'an nan su bullo da karin nau'o'in kayayyaki zuwa kasashen waje.

A fannin tsaro kuwa, har yanzu ana samun hare-haren ta'addanci a kasashen Najeriya da Somaliya. Kana yakin basasa da ya ki ci ya ki cinyewa a kasar Sudan ta Kudu ya tilastawa miliyoyin mutane barin muhallinsu. Wadannan lamura sun sa an fara nuna shakku kan karfin kungiyar AU a bangaren kau da rikici da tabbatar da tsaron nahiyar Afirka. Saboda haka akwai bukatar yiwa tsarin kungiyar gyaran fuska, ta yadda za ta iya daukar matakan da suka dace, da kara yin tasiri a al'amuran da suka shafi nahiyar Afirka.

Ban da haka kuma, idan aka nazarci al'ummomin nahiyar Afirka, za a ga cewa, kashi 60% na al'ummar nahiyar su biliyan 1.2 shekarunsu kasa da 24 ne a duniya. Hakan na nufin nahiyar tana da dimbin matasa, kana yawan al'ummarta za ta ci gaba da karuwa. Sai dai wannan yanayin da ake ciki yana bukatar kasashen Afirka da kungiyar AU da su dauki karin matakai, a kokarin samar da damammakin karatu da aiki ga matasansu.

A zamanin da muke ciki, zai yi wuya, wata kasa ta iya raya kanta ita kadai, ba tare da cudaya da mu'amala da sauran kasashe ba. Hakika kasashen Afirka da kasar Sin suna kara samun ci gaba a kokarinsu na hadin gwiwa da juna a shekarar 2017. Shawarar 'Ziri daya da Hanya daya' da kasar Sin ta gabatar ta neman inganta hadin gwiwa tsakanin kasashen duniya ita ma ta shafi kasashen Afirka, wadanda za su iya taka muhimmiyar rawa a cikin wannan shiri.

Kamfanin McKinsey mai ba da shawara kan harkokin tattalin arziki ya fitar da wani rahoto a watan Yunin bana, wanda ya nuna cewa, huldar ciniki tsakanin Afirka da Sin na samun ci gaba cikin sauri a shekaru 10 da suka wuce, inda yawan cinikayya tsakanin bangarorin 2 ya ke karuwa da kashi 20% a kowace shekara, kana yawan jarin da ake zubawa shi ma ya na karuwa da kashi 40% a duk shekara.

A nata bangaren, Madam He Wenping, wata masaniya a fannin ilimin huldar dake tsakanin Sin da Afirka ta kasar Sin, ta ce sabon tsarin zuba jari da kasar Sin ke gudanarwa a nahiyar Afirka, wato "gina kayayyakin more rayuwa" ya kara yadda "yankunan musamman na raya masana'antu", suke taka rawar a zo a gani a fannin raya tattalin arzikin kasashen Afirka.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China