in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sama da mutane biliyan 1 ne za su amfana da shirin inshoran manyan cututtuka na Sin
2017-12-18 09:44:20 cri

Hukumar lafiya da tsara iyali ta kasar Sin ta bayyana cewa, yanzu sama da Sinawa biliyan daya ne za su amfana da inshoran manyan cututtuka ta kasar.

Mataimakin shugaban hukumar Wang Hesheng shi ne ya bayyana haka, yana mai cewa, babban aikin dake gaban sashen lafiyar kasar a lokacin shirin raya kasa na shekaru biyar karo na 13 (2016-2020) shi ne inganta tsarin inshoran manyan cututtuka.

Mr Wang Hesheng ya kara da cewa, yayin da hukumar ke kokarin fadada shirin inshorar ta yadda mazauna birane da yankunan karkarar kasar za su amfana da shirin, a hannu guda su ma hukumomin lafiya sun rage adadin iyalan da za su biya inshoran, inda suka kara adadin kudi da masu cin gajiyar inshoran za su biya, sannan aka fadada hidimar inshorar.

Jami'in ya ce, yanzu inshoran manyan cututtukan tana kula da sama da kaso 50 cikin 100 na kudin maganin, kana a wasu yankunan karkarar kasar, tsarin yana kula da kaso 80 zuwa 90 cikin 100 na kudin maganin.

Hukumar ta ce, za ta yi kokarin ganin cewa, iyalai marasa karfi, da tsoffi da yara da masu nakasa ko cuttuttuka masu tsanani sun samu kyakkyawar kulawa.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China