Shugaban hukumar hadin gwiwar sanya-ido da kimanta ci gaba (JMEC) ta kasar Sudan ta kudu Festus Mogae ya yi kira ga shugabannin kungiyar raya kasashen gabashin Afirka ko IGAD a takaice, da su hada kansu, tare da yin magana da murya guda, kana su karfafawa jagororin Sudan ta kudu gwiwar amfani da wannan dama wajen dawo da shirin zaman lafiyar kasar bisa turba.
Mr Mogae ya yi wannan kiran ne a jiya Lahadi, cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai yayin taron ministocin kungiyar IGAD karo na 59 da ya gudana a birnin Addis Ababan kasar Habasha.(Ibrahim)