in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan mambobin kungiyar hadin kan kasa da kasa ta fuskar shirin talabijin bisa shawarar hanya daya da ziri daya ya kai 85
2017-12-15 13:52:05 cri

Jiya Alhamis a birnin Beijing, an yi taron koli na shekarar 2017 na dandalin tattaunawa tsakanin mambobin kungiyar hadin kan kasa da kasa ta fuskar shirye-shiryen talibijin, bisa shawarar hanya daya da ziri daya. Bisa labarin da muka samu daga wajen taron, an ce, ya zuwa yanzu, yawan mambobin kungiyar da ma abokanta ya kai wasu 85.

A ciki kuma, kawancen kasashen Asiya da tekun Fasific ta fuskar watsa labarai wato ABU, da hukumar ci gaban rediyo na yankin Asiya da tekun Fasific wato AIBD, sun zama abokan kungiyar masu samar da goyon baya, baya ga kawancen gidajen talibijin na kasashen da ke kan hanyar siliki, wadda ta zama abokiyar kungiyar a fannin hadin gwiwa.

Kungiyar hadin kan kasa da kasa ta fuskar shirye-shiryen talibijin bisa shawarar hanya daya da ziri daya, kawance ne na kafofin watsa labarai na kasa da kasa ta fuskar shirya fim da shirin talibijin, wanda aka kafa ta bisa shawarar da babban kamfanin shirye-shiryen talibijin na kasar Sin da gidan talibijin na kasar Sin suka gabatar, a yayin bikin shirye-shiryen rediyo da na talibijin na Larabawa da aka yi a farkon watan Mayun bara. Kungiyar ta kuwa kasance irinta ta farko a duk fadin duniya.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China