in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da bikin baje kolin hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka wajen samar da kayayyaki a Kenya
2017-12-15 10:50:46 cri

An kaddamar da bikin baje kolin hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, a fannin samar da kayayyaki na shekarar 2017 a birnin Nairobi fadar mulkin kasar Kenya a ranar 13 ga wannan wata.

Bikin baje kolin na yini hudu wanda hukumar sa kaimi kan cinikin kasa da kasa ta kasar Sin ta shirya ya shafi fannoni da dama; Misali fasahar sadarwa, da aikin gona, da gyara abinci, da samar da manyan kayayyakin more rayuwar jama'a, da gine-gine, da na'urorin aiki injiniya da sauransu.  

An kaddamar da bikin baje kolin hadin gwiwar tsakanin Sin da Afirka karo na farko a ranar 13 ga watan da muke ciki a birnin Nairobin kasar Kenya, bikin da ya samu halartar kamfanonin da suka zo daga larduna da birane da jihohin kasar Sin 17, da kuma yankin musamman na Hongkong da yawansu ya kai 60. Fadin filin da aka shirya bikin ya kai muraba'in mita 3000, kuma makasudin shirya bikin shi ne sa kaimi kan hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa a fannin samar da kayayyaki, tare kuma da taimakawa kasashen Afirka su samu ci gaba bisa dogaro da ikon kansu.

Kayayyakin da ake baje kolinsu a wurin na da yawan gaske, baya ga tarin mutane masu yawa da suka halarci taron.

Ngotho Gathu, manaja ne na wani kamfanin ba da shawara kan aikin gina manyan kayayyakin more rayuwar jama'a na kasar Kenya. A yayin bikin, ya bayyana cewa, "Bikin yana da ma'ana sosai, ina farin cikin ganin kamfanonin kasar Sin da yawan gaske da suka zo kasarmu don samar da kayayyaki, musamman ma a fannin samar da manyan kayayyakin more rayuwar jama'ar da nake sha'awa. Idan ba domin wannan bikin ba, mawuyaci ne a samu bayanai irin wadannan cikin gajeren lokaci. A saboda haka ina godewa wadanda suka shirya bikin, na riga na samu lambobin waya na kamfanonin kasar Sin da dama, nan gaba ina fatan za mu gudanar da hadin gwiwa tsakaninmu."

Xing Enyan, mataimakin manajan kamfanin kasar Sin ne reshin rukunin gina hanya na kasar Sin wato CCCC a yankin gabashin Afirka, yana shan aiki a bikin, ya yi mana bayani cewa, rukunin yana gudanar da aikinsa a Kenya har da tsawon shekaru 33, a cikin wadannan shekarun da suka gabata, rukunin yana gina hanyar mota da kadarko da kuma layin dogo da dama a kasar, a bayyane ne an lura cewa, yanayin sufuri da kasar Kenya ke ya yi manyan sauye-sauye, Xin Enyan ya ce, "A bayyane take cewa yanayin sufurin kasar Kenya ya samu manyan sauye-sauye, a baya birnin Nairobi yana fuskantar matsalar cunkuso mai tsanani, saboda babu hanyar mota da ke kewaye da birnin, amma yanzu an gina karkashin taimakonmu, kana layin dogon da ya hada Mombasa da Nairobi shi ma ya fara aiki, duk wadannan sun taimaka matuka wajen ci gaban tattalin arzikin kasar ta Kenya."

A sa'i daya kuma, kamfanin CCCC ya samar da guraben aikin yi da dama ga mazauna biranen kasar, yayin da yake gudanar da ayyuka, har ya sa GDPn kasar ya karu da kaso 1.5 bisa dari.

Ban da irin wannan aiki na gargajiya, kamfanonin kasar Sin suna kokarin yada fasahar samar da wutar lantarki da kuma sayar da na'urar zamani ta samar da wutar lantarki ga Kenya. Dalilin da ya sa haka shi ne domin ana ganin cewa, ya fi kyau a koya wa saura yadda ake kama kifi maimakon a rika ba da kifi, shi ya sa kamfaninin kasar Sin suna son koya wa aminan kasashen Afirka fasahohin da abin ya shafa kai tsaye ta hanyar gudanar da hadin gwiwa dake tsakanin sassan biyu.

Yanzu kasashen Afirka suna kokarin raya masana'antu, kasar Sin kuwa tana iya samar da taimako a fannonin fasaha da na'ura da kwararre da jari gare su, shi ya sa ana gudanar da hadin gwiwa tsakanin sassan biyu yadda ya kamata, babban wakilin asusun raya kasashen Afirka na kasar Sin dake Kenya Dong Fang yana ganin cewa, yanzu hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka a fannin samar da kayayyaki yana da babban karfi a asirce, ya ce, "Tattalin arzikin kasashen Afirka yana samun ci gaba cikin sauri, haka kuma suna bukatar jarin waje, da fasahar zamani, da kuma fasahar gudanar da harkokin kamfanoni. Kasar Sin kuwa tana da fiffiko a wadannan fannonin, don haka hadin gwiwa tsakaninsu zai amfani sassan biyu."

Ministan ma'aikatar masana'antu da ciniki da hadin gwiwa ta Kenya Adan Mohammed shi ma yana ganin cewa, bikin yana da babbar ma'ana, ya ce, "Muna farin cikin samun damar shirya wannan biki a kasarmu ta Kenya, domin bikin ya alamanta cewa, huldar sada zumunta da hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka, musamman ma tsakanin Sin da Kenya tana kara zurfafa kamar yadda ake fata."(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China