Yau Alhamis ne, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang ya bayyana a yayin taron manema labarai cewa, kasar Sin tana goyon baya a warware batun birnin Kudus bisa kudurin MDD da kuma matsayar da gamayyar kasa da kasa suka cimma kan batun. Kasar Sin tana fatan Isra'ila da Falesdinu za su hanzarta dawo wa kan teburin yin shawarwari, domin warware sabanin dake tsakaninsu yadda ya kamata.
Rahotanni na cewa, a jiya Laraba ne, mambobin kungiyar kasashen musulmi ta duniya (OIC) suka kira wani taro na musamman a birnin Istanbul na kasar Turkiya, inda suka zartas da wata sanarwa wadda ke yin kira ga gamayyar kasa da kasa da su amince da gabashin birnin Kudus a matsayin babban birnin Falesdinu. (Maryam)