Masana sun bayyana saurin karuwar kamfanoni masu jarin waje, a matsayin babban dalilin habakar alkaluman na FDI. Kaza lika kyawawan manufofin da mahukuntan kasar ke tsarawa, na taimakawa matuka wajen baiwa masu jarin waje karfin gwiwar samar da kudaden da ake bukata, wajen aiwatar da manyan ayyuka dake bukatar jarin waje.