Mr. Lounceny Fall wanda ya bayyana hakan ga mambobin kwamitin tsaron MDD a jiya Laraba, ya ce warware wadannan matsaloli na bukatar hadin gwiwa daga masu ruwa da tsaki daga yankin, da ma na kasa da kasa.
Jami'in ya ce a kasashen Chadi, da Gabon, da jamhuriyar Congo, matsanancin yanayin tattalin arziki, tare da matsaloli na siyasa tsakanin tsagin gwamnatocin kasashen da na 'yan adawa, na ci gaba da kasancewa abun damuwa.
Ya ce ga misali a Kamaru, rabin yankunan kasar na fama da matsalar tsaro mai nasaba da ayyukan kungiyar nan ta Boko Haram, da masu nasaba da rigingimun dake aukuwa a jamhuriyar Afirka ta tsakiya, da kuma ta 'yan aware dake yankuna masu magana da yaren Ingilishi.
A daya hannun kuma, jamhuriyar Afirka ta tsakiya na fama da hare hare daga kungiyoyin masu dauke da makamai, inda sau da yawa, ake hallaka jami'an MDD dake aikin wanzar da zaman lafiya, da masu aikin jin kai a kasar.(Saminu Alhassan)