Sanarwar da aka fitar a karshen taron kolin na wuni guda, wanda gamayyar kungiyar kasashen musulmi (OIC) ta shirya, ta bukaci dukkan kasashen musulmi na duniya su amince da tabbatar da kasar Palastinu kana su amince da gabashin Kudus a matsayin babban birnin Palastinawa.
Sanarwar ta ce, shugabanni da wakilan kasashen duniya da suka halarci taron sun yi Allah wadai da babbar murya da kuma bijirewa matakin da Amurkar ta dauka na kashin kanta, wanda shugaban kasar Donald Trump ya ayyana Jerusalem a matsayin babban birnin Israel.
Shugabannin sun bayyana matakin na Amurka a matsayin keta haddin al'ummar Palastinawa, da kuma yunkurin wargaza dukkan kokarin wanzar da zaman lafiya a yankin, da kuma kokarin haifar da bazuwar tsattsauran ra'ayin addini da ta'addanci, kana da yunkurin haddasa barazanar zaman lafiya da kwanciyar hankalin duniya baki daya.
Da yake jawabi a taron manema labarai a karshen taron kolin, shugaban Palastinawa Mahmoud Abbas yace, kasar Amurka ta nunawa duniya ba da gaske take yi ba game da yunkurin wanzar da zaman lafiya.(Ahmad)