in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta shirya bikin kasa na tunawa da kisan kiyashi na birnin Nanjing
2017-12-13 10:32:21 cri
A yau Laraba ne aka gudanar da bikin tunawa da kisan kiyashi na birnin Nanjing, domin nuna alhinin rasuwar Sinawan da suka rasa rayukan su a yayin kisan. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci bikin.

Bana an cika shekaru 80 da kisan kiyashi da aka yi a birnin Nanjing na kasar Sin. A ranar 13 ga watan Disamban shekarar 1937, sojoji mahara na kasar Japan suka kutsa cikin birnin Nanjing, inda suka shafe tsawon kwanaki sama da 40 suna kisan kiyashi. Bisa ga binciken da aka yi, fararen hula da fursunoni kimanin dubu 300 ne sojojin Japan suka kashe, a yayin da matan kasar Sin dubu 20 aka yi wa fyade, baya ga yadda sojojin Japan suka kone kaso daya daga cikin uku na birnin Nanjing.

A watan Faburairun shekarar 2014, hukumar dokoki ta kasar Sin ta zartas da kuduri, inda aka kebe ranar 13 ga watan Disamban ko wace shekara, a matsayin ranar duk kasa ta tunawa da 'yan kasar da aka kashe a yayin kisan kiyashi na birnin Nanjing.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China