in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An sake kiran taron koli game da tunkarar matsalar sauyin yanayi a Faransa
2017-12-13 11:08:33 cri

A jiya Talata 12 ga watan Disambar nan ne aka cika shekaru biyu da daddale yarjejeniyar tunkarar matsalar sauyin yanayi ta birnin Paris, a saboda haka aka sake gudanar da taron koli kan batun a kasar ta Faransa, taron mai taken "duniya guda daya" wanda ya gudana karkashin jagorancin shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron, da babban sakataren MDD Antonio Guterres, da shugaban bankin duniya Jim Yong Kim, ya samu mahalartan shugabannin kasashen duniya sama da 50, inda suka tattauna kan batun da ya shafi yadda za a tattara kudin warware wannan matsalar.

A karshen shekarar 2015, an zartas da yarjejeniyar tunkarar matsalar sauyin yanayi ta Paris, inda aka tsai da kuduri cewa, za a sanya kokari tare domin rage fitar da iskar gurbata muhalli bayan shekarar 2020, ta yadda za a cimma burin tunkarar matsalar sauyin yanayi.

Duk da cewa, an daddale yarjejeniyar, amma ba a tabbatar da batutuwan da aka tattauna yadda ya kamata ba, ya zuwa watan Yunin bana, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sanar da cewa, kasarsa za ta fice daga yarjejeniyar, hakan ya sa yarjejeniyar ta kara fuskantar kalubale, shugaban Faransa Macron shi ma ya bayyana cewa, a halin da ake ciki, an gamu da babbar matsala yayin da ake aiwatar yarjejeniyar, shi ya sa ya zama wajibi a dauki mataki nan take, Macron ya ce, "Muna fama da kalubale mai tsanani mai yiwuwa kokarinmu zai bi ruwa, mun gani ba mu samu ci gaba kamar yadda muke fata ba, shi ya sa kamata ya yi mu dauki mataki ba tare da bata lokaci ba, abu mai faranta ran mutane shi ne mun lura da matsalar gaza samun sakamako."

A ranar 11 ga wata, yayin da Macron ya yi zantawa da manema labarai, ya bayyana cewa, ya kamata Trump ya sauke nauyin tarihi bisa wuyansa, shi ma ya bayyana cewa, yana cike imani cewa, Trump zai sauya ra'ayinsa kan batun, kana ya nuna maraba ga Amurka da ta sake shiga yarjejeniyar Paris, ban da haka Macron ya jaddada cewa, an shirya wannan taron kolin a jiya ne ba domin tattara kudi kawai ba, sai dai ana sa ran za a samu wasu hakikanan hanyoyin rage fitar da iskar gurbata muhalli.

Bisa alkaluman da hukumar makamashin duniya ta samar, an ce, domin cimma burin kayyaden zafin yanayin da aka tsara a cikin yarjejeniyar Paris, za a zuba jarin da ya kai dalar Amurka biliyan 3500 a fannin samar da makamashi a ko wace shekara a cikin shekaru 30 masu zuwa, an shirya wannan taron kolin ne domin neman samun kudaden da ake bukata, babban sakataren MDD Guterres shi ma ya gabatar da bukatarsa ga shugabanni mahalartan taron, ya ce, "Yanzu kusan kowanen birni a fadin duniya yana kokari matuka domin tunkatar da matsalar sauyin yanayi, saboda kowa ya san aikin yana da muhimmanci kwarai ga makomar bil adama, muna fatan za a aiwatar da yaryejeniyar Paris lami lafiya, a nan bari na gayyaci daukacin gwamnatocin kasashen duniya su kara ba da gudumowarsu kan batun."

Yayin taron, wakilin musamman kan harkokin tunkarar matsalar sauyin yanayi na gwamnatin kasar Sin Xie Zhenhua ya yi bayani kan yanayin da kasar Sin ke ciki wajen tunkarar matsalar, shi ma ya yi bayani kan rawar da gwamnatin kasar ke takawa a fannin, ya ce, "Da farko, tsara manufofin tunkarar matsalar sauyin yanayi a dogon lokaci. Na biyu, gwamnatin kasar ta fitar da manufofin da suka dace domin aiwatar da tsarin da aka kafa, misali manufofin farashi da haraji da kuma kudi. Na uku, gwamantin kasar ta kara mai da hankali kan amfanin kasuwa. Na hudu, a kebe wasu kudaden da aka tattara domin gudanar da hadin gwiwar dake tsakanin kasashe masu tasowa."

Bisa matsayinsa na manzon musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping, mataimakin firayin ministan majalisar gudanarwar kasar Ma Kai ya gabatar da wani jawabi yayin taron da aka kira a yammacin jiya, inda ya sake jaddada cewa, gwamnatin kasar Sin tana goyon bayan yarjejeniyar Paris, ita ma za ta ci gaba da shiga hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa kan aikin tunkarar matsalar sauyin yanayi, ya ce, "Tunkarar matsalar sauyin yanayi da rage fitar da iskar gurbata muhalli, ba aiwatar da yarjejeniyar kasa da kasa kawai ba, kasar Sin ita kanta ta zabi hanyar samun dauwamammen ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba. Nan gaba kasar Sin za ta ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar Paris, ta yadda za a cimma burin tabbatar da al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil adama."

Bisa labarin da fadar shugaban Faransa ta bayar, an ce, an samu sakamako a fannoni 12 yayin taron kolin yini guda, wadanda ke shafar kara tattara kudi domin nuna goyon baya ga kasashen duniya wajen tunkarar matsalar sauyin yanayi da hanzarta raya tattalin arziki ba tare da gurbata muhalli da kuma shigar da matsalar yanayi cikin tsarin kudi da manufofin gwamnatin kasa da sauransu.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China