in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan kasuwancin Sin ya gabatar da jawabi a taron ministocin WTO karo na 11
2017-12-12 11:11:08 cri

Yanzu haka ana gudanar da taron ministocin kungiyar ciniki ta duniya wato WTO karo na 11 a Buenos Aires, fadar mulkin kasar Argentina. Ministan kasuwancin kasar Sin Zhong Shan na cikin halarta cikakken taron da aka gudanar da safiyar jiya Litinin, tare da sauran wakilan tawagar gwamnatin kasar Sin, inda ya kuma gabatar da jawabi.

A cikin jawabin da ya gabatar jiya, ministan kasuwancin kasar Sin Zhong Shan ya yi nuni da cewa, har kullum kasar Sin tana goyon bayan yunkurin habaka cudanyar tattalin arzikin kasashen duniya, da tsarin ciniki tsakanin bangarori da dama, kana kasar Sin tana son sanya kokari matuka tare da sauran mambobin kungiyar cinikin duniya domin sa kaimi kan ci gaban tattalin arziki a fadin duniya, ya ce, "Yunkurin habaka cudanyar tattalin arzikin kasashen duniya, ya dace da yanayin da muke ciki yanzu, haka kuma ya taka muhimmiyar rawa wajen karuwar tattalin arzikin duniya. Amma yayin da muke kokari tare, muna fuskantar kalubale, wato wasu kasashe suna nuna ra'ayin ba da kariya ga cinikayya. Muna ganin cewa, ba zai yiyu wata kasa ta iya samun ci gaba bisa karfin kanta kadai ba, kuma babu wadda ya dace ta taka rawa a madadin kungiyar ciniki ta duniya, a saboda haka, ya zama wajibi mu yi kokari tare, domin kara habaka cudanyar tattalin arzikin duniya ba tare da rufa rufa ba, ta yadda za mu cimma burin amfanar da daukacin kasashen duniya baki daya."

Zhong Shan ya jaddada cewa, kasar Sin tana son nuna goyon baya ga daukacin kasashen duniya, musamman ma ga kasashen dake fama da tsananin talauci, ta yadda za su shiga tsarin ciniki tsakanin bangarori da dama, ya ce, "Kasar Sin ta samar da kudin taimako ga asusun yarjejeniyar saukaka sharadin ciniki domin taimakawa mambobin kungiyar ciniki ta duniya, wadanda ke bukatar taimako yayin da suke kokarin tabbatar da shawarwarin ciniki, kuma kasar Sin ta riga ta daddale takardar tunatarwar hadin gwiwa tare da ofishin sakatariyar kungiyar ciniki ta duniya, game da gudanar da aiki a mataki na 7 na 'shirin kasar Sin' domin samar da taimako ga kasashen dake fama da tsananin talauci, ta yadda za su shiga tsarin ciniki tsakanin bangarori da dama. Haka kuma su samu damar shiga babban iyalin nan na kungiyar WTO."

Kana minista Zhong Shan ya yi bayani kan bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa na kasa da kasa na kasar Sin, karo na farko da za a gudanar da shi a birnin Shanghai a shekara mai zuwa ga mahalartan cikakken taron, inda ya bayyana cewa, "Za a gudanar da bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa na kasa da kasa na kasar Sin karo na farko a birnin Shanghai dake kudancin kasar Sin a watan Nuwamban shekarar 2018 dake tafe, wannan shi ne hakikanin matakin da kasar Sin ta dauka, domin sa kaimi ga yunkurin habaka cudanyar tattalin arzikin duniya, tare kuma da tabbatar da ciniki maras shinge, wannan ma muhimmin mataki ne da kasar Sin ta dauka a fannin bude kofa ga kasuwannin kasashen duniya. Ko shakka babu matakin zai taka rawa wajen tabbatar da ci gaban tattalin arzikin duniya.

Ban da haka kuma, kasar Sin za ta samar da hidima mai inganci ga kasashen da za su halarci bikin, musamman ma ga kasashe masu tasowa, da kasashen dake fama da tsananin talauci. Kaza lika, za a shirya dandalin ciniki na kasa da kasa na Hongqiao yayin bikin baje kolin, inda za a tattauna kan batutuwan dake shafar cinikayya tsakanin kasashen duniya, da kuma zuba jari da sauransu. Muna fatan kasashen duniya za su halarci bikin."

Babban jami'in hukumar cinikin duniya Roberto Azevedo ya yi nuni da cewa, shirya bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa na kasa da kasa a kasar Sin ya nuna mana cewa, kasar Sin tana kokarin taimakawa kasashe masu tasowa wajen kara karfinsu na gudanar da ciniki, kana ya nuna cewa, kasar Sin tana aiwatar da manufar amfanar juna, da kuma samun moriya tare. Wasu ministocin kasuwanci mahalartan taron sun yaba wa kasar Sin sosai saboda goyon baya da gatanci da take samarwa kasashe masu tasowa, da kasashen dake fama da talauci, suna ganin cewa, lamarin ya shaida cewa, kasar Sin babbar kasa ce mai sauke nauyin dake wuyanta a harkokin duniya, su ma sun bayyana cewa, suna fatan za su yi amfani da wannan sabon dandalin hadin gwiwa na kasa da kasa, wato bikin baje kolin da za a gudanar a birnin Shanghai a shekara mai zuwa, ta yadda za su kara habaka hadin gwiwar tattalin arziki, da ciniki tsakanin kasashensu da kasar Sin.

An kaddamar da taron ministocin kungiyar cinikayya ta duniya karo na 11 na tsawon kwanaki hudu ne a ranar 10 ga wannan wata a birnin Buenos Aires na kasar Argentina, inda ake tattaunawa game da aikin hukumar a sabon zamanin da ake ciki.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China