Mai magana da yawun sojin ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, an gano wasu rokoki biyu da aka harba da yammacin ranar ta Litinin. Sai daga ba'a gano ko harin ya yi barna ba, kakakin sojin ya kara da cewa, dakarun sojin suna cigaba da bincike a yankin, domin gano burburshin rokokin da aka harba yankin.
Kasa da sa'a guda daga bisani, tankokin yakin Isaraila da jiragen saman yaki sun kutsa zuwa yankin zirin Gaza. Sun kaddamar da hare hare kan dakarun kungiyar Hamas dake kudancin zirin Gaza, inji kakakin sojin Isra'ilan.
Babu wata kungiya data yi ikirarin kaddamar da harin rokar wanda bai kai ga nasara ba, sai dai dakaraun sojin sunce sun dora alhakin duk wani tashin hankali da ya barke a zirin Gaza kan magoya bayan Hamas.
A kalla rokoki uku aka harba kan dakarun sojin a kudancin Israila a karshen mako, amma bai haddasa wata barna ba, amma sojojin Isra'ilan sun hallaka mutane 4 a zirin Gaza, inji kafafen yada labaran Palastinu.(Ahmad Fagam)