in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta yi tir da harin da aka kai wa rundunar kare zaman lafiya ta MDD dake Congo (Kinshasa)
2017-12-11 20:00:39 cri

Yau Litinin ne, Lu Kang ya bayyana a yayin taron manema labaru da aka saba shiryawa a nan Beijing cewa, kasar Sin ta yi tir da harin da aka kai wa rundunar kiyaye zaman lafiya da MDD ta jibge a kasar Congo (Kinshasa).

Kasar Sin tana son taka rawa don ganin an warware batun Congo (Kinshasa) cikin ruwan sanyi da kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a nahiyar Afirka.

A daren ranar 7 ga wata ne, bisa agogon wurin, an kai hari kan rundunar kiyaye zaman lafiya ta MDD a lardin arewacin Kivu da ke gabashin Congo (Kinshasa), harin da ya haddasa rasuwar sojojin kiyaye zaman lafiya na MDD 'yan kasar Tanzania su 15, da sojojin Congo (Kinshasa) su 5. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China