in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD: Cikin shekaru 2 tashe tashen hankula sun sabbaba kisan mutane sama da 2,000 a Somalia
2017-12-11 10:15:00 cri

A kalla fararen hula 2,078 ne suka rasa rayukan su, baya ga wasu 2,507 da suka jikkata, sakamakon tashe tashen hankula daban daban da suka auku a kasar Somalia, tsakanin watan Janairun shekarar 2016 zuwa watan Oktobar bana.

Wani rahoton hadin gwiwa da MDD ta fitar a jiya Lahadi, ya nuna cewa tashe tashen hankulan na da nasaba ne da kungiyar 'yan ta'adda ta Al-Shabaab, wadda ke amfani da makamai domin kaddamar da hare hare.

Rahoton wanda ofishin MDD mai lura da kare hakkokin bil Adama da ofishin tawagar wanzar da zaman lafiya na MDD mai aiki a Somalia ko UNSOM a takaice suka tsara, ya ce kaso 60 bisa dari na mace macen da aka samu, na da nasaba ne da hare haren kungiyar Al-Shabaab, sai kuma kaso 13 bisa dari dake da alaka da masu dauke da makamai na wasu kabilun kasar. Yayin da kaso 11 bisa dari ya shafi wasu jami'an hukumomin tsaro kamar sojoji da 'yan sanda.

Kaza lika rahoton ya nuna cewa, kaso 4 bisa dari na wannan adadi na da nasaba da dakarun dake aikin wanzar da zaman lafiya a kasar, karkashin inuwar kungiyar hadin kan Afirka ta AU ko AMISOM a takaice, baya ga wani kaso 12 bisa dari wanda mahara da ba a tantance ko su waye ba suka kaddamar.

Wakilin musamman na babban magatakardar MDD a Somalia Michael Keating, ya ce dukkanin masu ruwa da tsaki a tashe tashen hankulan dake wakana a Somalia, ba sa daukar matakan da suka wajaba, na kare salwantar rayukan fararen hula.

Mr. Keating ya ce, baya ga asarar rayuka, tashe tashen hankula sun lalata dunbin ababen more rayuwa a Somalia, tare da raba dubban 'yan kasar da muhallan su, sun kuma haifar da bukatar gudanar da ayyukan jin kai ga al'ummu da dama.

Rahoton ya kuma bayyana yadda tashe tashen hankula a Somalia suka shafi rayukan yara kanana masu tarin yawa, ciki hadda kusan yara 3,335 da aka shigar ayyukan soja cikin watanni 10 na farkon shekarar 2017.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China